Hukumar yan sandan Najeriya ta samu nasarar damke wasu masu garkuwa da mutane 13 da suka addabi jihar Katsina wanda ya kai ga sace surukar gwamnan jihar, Aminu Bello Masari a ranar 8 ga watan Fabrairu, 2019.
Kwamishanan yan sandan jihar Katsina, ya bayyanasu ga manema labarai a yau Litinin, 20 ga watan Mayu, 2019. Jawabin yace:
"Sakamakon garkuwa da surukar gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, a ranar 8 ga Febraoru, 2019 a gidanta dake Katsina, jami'an rundunar IRT karkashin atisayen Operation Puff Adder sun kaddamar da sintirin nemo yan barandan.
Jami'an sun samu nasarar damke masu garkuwa da mutanen tare da mai sayar musu makamai inda suka bayyana ayyukan fashi da makamin da suka aikata a jihar Katsina.

Da duminsa
Source: Facebook
KU KARANTA: Jirgi kirar Boeing 747 jibge da makamai ya dira Najeriya
Masu garkuwa da mutanen sune :
1) Abdullahi M. Sani
2) Abubakar Dani dan unguwar Sabuwar Unguwa
3) Marwana Gide dan garin Yan Maiwa
4) Rabe Hamza aka Tankabaje dan kauyen Nasarawa Bugaje
5) Abdulkarim Aliyu
6) Musa Yakubu
7) Abubakar Abdullahi
8 Napkon Sambo, dan garin Jos mai sama musu makamai
9) Haruna Adamu , direban makamai
10) Taiwo Abayomi 28yrs
11) Ali Samaila
12) Abubakar Sulaiman
13) Ibrahim Bille
Daga cikin makaman da aka kama sune:
Bindigar AK47 rifle,
Carbin harsasai 22
Harsasan Ak47 1,000 da sauransu."

Da duminsa: An damke masu garkuwa da mutane 13 da suka sace surukar gwamnan jihar Katsina (Hotuna)
Source: Facebook
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Da duminsa: An damke masu garkuwa da mutane 13 da suka sace surukar gwamnan jihar Katsina (Hotuna)
Source: Facebook