Shugaba Trump yace Amurka za ta ga bayan Iran idan aka takulo ta

Shugaba Trump yace Amurka za ta ga bayan Iran idan aka takulo ta

Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya sake jawo abin magana a Duniya bayan da ya fara tabo kasar Iran a irin maganganunsa da ya saba. Trump ya ja kunnen kasar da ta bi a hankali da Amurka.

Donald Trump ya aikawa Iran wannan gargadi ne a shafinsa na Tuwita Ranar Asabar 18 ga Watan Mayu. Shugaba Trump ya nuna cewa kasar Amurka za ta murkushe Iran a daina jin duriyar ta har abada idan ta cigaba da shige mata gaba.

“Idan har Iran tana neman takulo mu fada, to karshen ta ya zo kenan…”

Shugaban na Amurka a shafin na sa na Tuwita ya fadawa Iran din da ta guji yi wa kasar Amurka wata barazana. Donald Trump din yana mai nuna cewa muddin Iran tana da shirin yakar Amurka ne, to ita ma kasar a shirya take tsaf a yanzu.

Trumop ya karasa rubutun na sa da:

“…Ka da ku sake yi wa Amurka wata barazana!”

KU KARANTA: Wani jirgi ya shigo Najeriya makil da makamai

Shugaba Trump yace Amurka za ta ga bayan Iran idan aka takulo ta

Trump ya gargadi Kasar Iran da ta shiga taitayinta a Tuwita
Source: UGC

Sai dai a lokacin da aka yi hira da shugaban na Amurka, Trump, a gidan talabijin na Fox News daga baya, yayi la'asar inda yace ba za su taba kyale Iran ta rika neman takulo fada a Duniya ba.

"Ba ni da sha’awar yaki. Amma babu yadda za ayi mu zurawa irin su Iran idanu, ba za su mu taba bari kasar Iran ta mallaki makaman kare-dangi ba, ba za ta taba yiwuwa ba.” Inji Donald Trump.

Babban Sojan kasar Iran, Manjo Janar Hossein Salami, yace Iran ba ta da niyyar yaki da kowa, amma Hafsun Sojin yace idan aka kawowa Kasar farmaki, za su tashi tsaye su kare martabar kasar.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel