Manyan Sanatoci sun ja daga wajen takarar Lawan da Ndume

Manyan Sanatoci sun ja daga wajen takarar Lawan da Ndume

Yayin da makonni 3 kadai su ka rage a zabi shugabannin majalisar tarayya a Najeriya, mun samu labari cewa har yanzu ana ta faman rikici tsakanin Magoya bayan wadanda ke takarar wadannan kujeru.

Sanatocin da ke tare da Ahmad Lawan da kuma wadanda ke bayan Mohammed Ali Ndume su na samun ja-in-ja ne a kan yadda za ayi zaben wannan karo. Magoya bayan Sanata Ahmad Lawan su na so ayi zaben ne a fili ido-na-ganin-ido.

A wani bangare, wadanda ke tare da Sanata Mohammed Ali Ndume, su na kokarin ganin an cigaba da amfani da tsarin da aka yi amfani da shi a zaben 2015. A wajen zaben wancan karo, ‘yan majalisun kasar sun kada kuri’ar su ne a asirce.

Wani ‘Dan majalisa ya fadawa Jaridar The Sun cewa rikakkun ‘yan majalisar da ke tare da APC su na kokarin tursasawa majalisar wajen ganin an yi zaben a bainar Duniya. Wadannan ‘yan majalisa za su yi amfani ne da fadar shugaban kasa.

KU KARANTA: Wani Jagoran APC a Legas yayi kaca-kaca El-Rufai yace ya daina shisshigi

Sanata Aliyu Sabi Abdullahi, wanda yake tare da Ahmad Lawan ya karyata wannan batu tuni, inda yace akwai manyan abubuwa da ke gabansu. A halin yanzu dai Ahmad Lawan da kuma Ali Ndume kurum ake jin duriyarsu a wannan takarar.

Shi kuma wani wanda yake goyon bayan Ali Ndume yace za ayi amfani ne da tsarin da ake tafiya a kai tun 2015 na yin zabe a boye. Sanatan yace idan har ba a sauya tsari ba, Sanata Ahmad Lawan da Mabiyansa za su sake shan kashi.

‘Dan majalisar ya kuma kara da cewa ana kokarin yin amfani da EFCC domin kama wasu Sanatocin da ba su tare da Ahmad Lawan a lokacin zaben. Wannan ne ma ya sa aka kama wani Sanatan PDP aka nemi a garkame har bayan zabe.

Ana kuma rade-radin cewa akwai masu shirin tada rikici a majalisar idan abubuwa ba su tafi yadda su ke so ba. Sanatocin dai sun musanya wannan zargi inda su kace babu wanda yake da wannan nufi.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel