INEC ta janye takardun shaidar cin zabe na yan takara 25

INEC ta janye takardun shaidar cin zabe na yan takara 25

Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) tace ta janye takardun shaidar cin zabe 25 da ta baiwa wasu yan takarar da suka lashe zabe a lokacin zaben kasa na 2019, biyo bayan umurnin kotu.

Shugaban kwamitin bayanai da wayar da kan masu zabe, Mista Festus Okoye, ya bayyana hakan a wani taro kan gudanar kafofin watsa labarai a zaben 2019 wanda ya gudana a Enugu a ranar Litinin, 20 ga watan Mayu.

Okoye ya bayyana cewa 20 daga cikin takardun shaidar cin zaben 25 an janye su ne daga mambobin jam’iyyar All Progressive Congress (APC) zuwa ga wasu mambobin APC, yayinda aka janye biyu daga mambobin People Democratic Party (PDP sannan aka mika su ga wasu mambobin na PDP.

INEC ta janye takardun shaidar cin zabe na yan takara 25

INEC ta janye takardun shaidar cin zabe na yan takara 25
Source: Instagram

Ya bayyana cew an janye sauran ukun ne daga mambobin APC da PDP, sannan aka mika su ga wasu jam’iyyun siyasa.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Gwamnatin tarayya ta kaddamar da 29 ga Mayu da 12 ga Yuni a matsayin ranakun hutu

“Kafin mu bar hedkwatar INEC na kasa a ranar Juma’a, hukumar ta janye takardun shaidar cin zabe 25 daga mammalakansu na karko sannan ta mika su ga wasusabbin mutane biyo bayan umurnin kotu da ta umurce ta da yin hakan, inji shi.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel