Shehin Malamin Izala, Mustapha Konduga ya riga mu gidan gaskiya

Shehin Malamin Izala, Mustapha Konduga ya riga mu gidan gaskiya

A bisa al'ada ta rayuwa da kowane mai rai sai ya dandani mutuwa, mun samu cewa fitaccen shehin malamin nan na Izala wanda kuma ya kasance sakataren kungiyar JIBWIS (Jama'atul Izalatul Bid'a Wa Iqamatus Sunna), Sheikh Ali Mustapha Kondogu ya riga mu gidan gaskiya.

Shehin Malamin Izala, Sheikh Ali Mustapha Konduga

Shehin Malamin Izala, Sheikh Ali Mustapha Konduga
Source: UGC

Shugaban kungyar JIBWIS reshen jihar Borno, Sheikh Babagana Abdu, shi ne ya bayar da shaidar hakan da cewar Marigayi Shehin Malami Konduga, ya riga mu gidan gaskiya da safiyar yau ta Litinin bayan ya sha fama da wata 'yar takaitacciyar rashin lafiya da ta zamto ajalin sa.

Shakku babu marigayi Malam Konduga ya cika a asibitin koyarwa na jami'ar Maiduguri dake jihar Borno a ranar Litinin da tayi daidai da ranar 15 ga watan Ramadana, kwanaki uku bayan kwanciyar sa jinya.

An haifi marigayi Sheikh Konduga a shekarar 1968 inda ya kasance Almajiri da ya fara daukan karatu na darussan ilimi daban-daban a wurin Mallam Awa Sangaya. Bayan haddace mafificin Littafi na Al-Qur'ani, ya fara karatun sa na firamare da kuma matakin sakandire zuwa kwaleji a fannin nazarin addinin Musulunci.

KARANTA KUMA: Kakakin Majalisar Wakilai: Buhari na goyon bayan Kudu maso Gabas

A shekarar 2002, Marigayi Konduga ya halarci jami'ar Musulunci dake birnn Madina a kasa ma tsarki inda ya kammala karatun digiri na farko. Ya kammala karatun digiri na biyu a jami'ar Jos da ke jihar Filato yayin da ya kuma karkare digirin digir gir a jami'ar jihar Nasarawa a shekarar 2006.

Yayin da ya riga mu gidan gaskiya bayan Mai Duka ya azurta shi da 'ya'ya goma sha biyar da ya samu ta hanyar Iyalan sa uku, za kuma a gudanar da jana'izar sa da misalin karfe 4.00 na Yammacin Litinin a babban masallacin unguwar gidaje 707 dake birnin Maiduguri.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta a Facebook ko kuma Twitter:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi:

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel