Yanzu Yanzu: Gwamnatin tarayya ta kaddamar da 29 ga Mayu da 12 ga Yuni a matsayin ranakun hutu

Yanzu Yanzu: Gwamnatin tarayya ta kaddamar da 29 ga Mayu da 12 ga Yuni a matsayin ranakun hutu

Gwamnatin tarayya a ranar Litinin, 20 ga watan Mayu, ta kaddamar da ranar Laraba, 29 ga watan Mayu da kuma 12 ga watan Yuni a matsayin ranakun hutu domin bikin rantsar da Shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma ranar Damokradiyya.

Ministan labarai, Alhaji Lai Mohammed ne ya sanar da hakan a wani taron manema labarai gabannin rantsar da Shugaban kasa Muhammadu Buhari a karo na biyu.

Da yake ci gaba da bayani, Lai Mohammed yace duk mutanen da ke muradin ganin an gayyace su zuwa wajen bikin rantsar da Shugaban kasar, za a gayyace su zuwa bikin ranar Damokradiyya.

“Duk wadanda ke son a gayyace su bikin rantsar da Shugaban kasa za a gayyace su bikin ranar 12 ga watan Yuni wato bikin damokradiyya." Muryar Najeriya ta ruwaito.

A halin da ake ciki, Legit.ng ta rahoto a baya cewa, Shugaba Muhammadu Buhari na shirin baiwa yan Najeriya a mamaki a sabuwar gwamnatin da zai nada musamman sabuwar ranar Demokradiyya 12 ga Yuni. Ana kyautta zaton cewa nan da ranar 29 ga Mayu, wasu sunayen zasu fara bayyana.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Buhari ya amince da nadin Yadudu a matsayin sabon manajan darakta na FAAN

Majiyar Aljazirah ta bayyana cewa shugaba Muhammadu Buhari na shirin nada tsohon gwamnan jihar Legas a zamanin mulkin soja, Janar Buba Marwa ko kuma tsohon shugaban hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zabon kasa wato EFCC, Nuhu Ribadu.

Daya daga cikinsu zai maye kujerar Abba Kyari, mai ci a yanzu.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Online view pixel