Yanzu Yanzu: Buhari ya amince da nadin Yadudu a matsayin sabon manajan darakta na FAAN

Yanzu Yanzu: Buhari ya amince da nadin Yadudu a matsayin sabon manajan darakta na FAAN

Rahotanni sun kawo cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin Kyaftin Rabiu Hamisu Yadudu a matsayin sabon manajan darakta na hukumar kula da filayen jirgin sama na tarayya (FAAN).

A cewar jaridar Leadership, Kyaftin Yadudu zai karbi aiki ne daga tsohon manajan darakta, Injiniya Saleh Dunoma.

Legit.ng ta tattaro cewa an sanar da sabon nadin ne a wani jawabi da mataimakin daraktan labarai da harkokin jama’a na ma’aikatar sufuri (jirgin sama), James Osausu ya saki a ranar Litinin, 20 ga watan Mayu.

Yanzu Yanzu: Buhari ya amince da nadin Yadudu a matsayin sabon manajan darakta na FAAN

Yanzu Yanzu: Buhari ya amince da nadin Yadudu a matsayin sabon manajan darakta na FAAN
Source: Facebook

Kyaftin Yadudu ya kasance kwararren ICAO/ACI na tashar jirgin sama na kasa da kasa. Har zuwa nadinsa, ya kasance daraktan ayyukan filin jirgi na hukumar.

Nadin nashi zai fara aiki ba tare da bata lokaci ba.

KU KARANTA KUMA: Mataimakin Shugaban kasa Osinbajo ya jagoranci zaman majalisar zartarwa, hotuna

A wani lamari na daban, mun ji cewa an fara shirin fafatawa a game da wanda zai zama Ministan gwamnatin tarayya daga jihar Kwara inda manyan ‘yan siyasan da ake ji da su a jihar su ka kunno-kai.

A halin yanzu Magoya-bayan Sanata Gbemisola Saraki sun budo wuta, yayin da Masoyan Alhaji Lai Mohammed a wani bangaren, su ke ganin da su za a sake komawa gwamnatin shugaba Buhari.

Gbemisola Saraki, ‘Diya ce wajen babban ‘Dan siyasar da aka yi a Kwara watau Marigayi Sanata Olusola Saraki. Shi kuma Lai Mohammed yana cikin manyan tafiyar APC tun a lokacin kafuwarta.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit Nigeria

Tags:
Mailfire view pixel