Mataimakin Shugaban kasa Osinbajo ya jagoranci zaman majalisar zartarwa, hotuna

Mataimakin Shugaban kasa Osinbajo ya jagoranci zaman majalisar zartarwa, hotuna

- Mataimakin Shugaban kasa Yemi Osinbajo ya jagoranci zaman majalisar zartarwa a fadar Shugaban kasa

- An gudanar da taron a yau Litinin sabanin yadda yake gudana a ranar Laraba, duk a cikin kokarin da ake yi na ganin an kare gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari mai ci a cikin nasara

- Za a sake rantsar da Shugaban kasa Muhammadu Buhari a karo na biyu a ranar 29 ga watan Mayu

A yanzu haka mataimakin Shugaban kasa Yemi Osinbajo na kan jagorantar zaman majalisar zartarwa a fadar Shugaban kasa da ke Villa, Abuja.

An fara taron ne da misalin karfe 10:02 na safe inda aka fara da rera taken kasar.

Ministan ruwa Suleiman Adamu ne ya gabatar da addu’an Musulunci yayinda ministan harkokin Niger Delta, Usani Usani ya gabatar da na Kirista.

Mataimakin Shugaban kasa Osinbajo ya jagoranci zaman majalisar zartarwa, hotuna

Mataimakin Shugaban kasa Osinbajo ya jagoranci zaman majalisar zartarwa, hotuna
Source: Facebook

Taron da aka gudanar a yau Litinin, 20 ga watan Mayu kan gudana ne a duk ranar Laraba, sai dai hakan na daga cikin kokarin da ake yi na ganin an kare gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari mai ci a cikin nasara.

Za kuma a sake gabatar da zaman a ranar Laraba.

Mataimakin Shugaban kasa Osinbajo ya jagoranci zaman majalisar zartarwa, hotuna

Mataimakin Shugaban kasa Osinbajo ya jagoranci zaman majalisar zartarwa, hotuna
Source: Facebook

KU KARANTA KUMA: Zaben gwamnan Kano: Ganduje zai gabatar wa kotu kundi mai shafi 1,800

Mataimakin Shugaban kasa Osinbajo ya jagoranci zaman majalisar zartarwa, hotuna

Mataimakin Shugaban kasa Osinbajo ya jagoranci zaman majalisar zartarwa, hotuna
Source: Facebook

Mataimakin Shugaban kasa Osinbajo ya jagoranci zaman majalisar zartarwa, hotuna

Mataimakin Shugaban kasa Osinbajo ya jagoranci zaman majalisar zartarwa, hotuna
Source: Facebook

A halin da ake ciki, ana shirye-shiryen sake rantsar da Shugaban kasa Muhammadu Buhari a karo na biyu a ranar 29 ga watan Mayu.

Sai dai a halin yanzu Shugaban kasar na a kasa mai tsarki inda yake gudanar da aikin Umrah.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel