Tabbas muna binciken Okorocha - Magu

Tabbas muna binciken Okorocha - Magu

Hukumar yaki da cin hanci da karya tattalin arziki (EFCC) ta tabbatar da cewar ta na gudanar da bincike a kan gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha.

Mukaddashin shugaban hukumar EFCC na kasa, Ibrahim Magu, ne ya bayar da wannan tabbacin yayin wata gana wa da gidan Talabijin na Channels a Landan.

Da aka tambaye shi ko hukumar sa na gudanar da abincike a kan gwamna Rochas, sai ya kada baki; "kwarai kuwa."

"Tabbas, mu na gudanar da bincike a nan da can. Mu na binciken kusan kowa da kowa," a cewar Magu.

Ya bayyana cewar hukumar EFCC ba ta fitar da sanar wa dangane da binciken da take gudanar wa ba tare da ya kai wani mataki ba.

Magu ya ce hukumar na yin hakan ne domin kare duk wani yunkuri ko shiga hanci da kan iya kawo cikas a binciken da take yi.

Tabbas muna binciken Okorocha - Magu

Rochas Okorocha
Source: Getty Images

A cewar sa, gwamna Okorocha na daya daga cikin dumbin mutanen da hukumar ke kan gudanar da bincike a kan su.

Shugaban na EFCC na ya kara da cewa yana sane da wasu rahotanni dake yawo a kafafen sada zumunta a kan binciken, ya kara da cewa bayanan da hukumar ke da su sun sha banban da wadanda ake yada wa a irin wadannan kafafe.

DUBA WANNAN: Rundunar 'yan sanda ta kama masu garkuwa 7, AK47 4 da carbin alburusai a cikin sa'o'i 24

Sai dai, ya ki ya yi karin haske a kan binciken.

Magu ya ziyarci kasar Ingila domin gana wa da masu bincike dake taimakon Najeriya wajen bankado almundahanar kudade da fitar da su zuwa kasashen ketare.

A 'yan kwanakin baya bayan nan ne, gwamna Okorocha ya koka a kan cewar hukumar EFCC na bin diddigin al'amuran sa, ya kara da cewa shine gwamnan da aka fi bincika a kasar nan.

Rochas ya yi zargin cewar wasu abokan hamayyar sa a siyasance ne ke shirya masa makarkashiya domin su ga bayan sa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel