Sabon gwamnati: Buba Marwa ko Nuhu Ribadu zasu maye kujeran Abba Kyari

Sabon gwamnati: Buba Marwa ko Nuhu Ribadu zasu maye kujeran Abba Kyari

Shugaba Muhammadu Buhari na shirin baiwa yan Najeriya a mamaki a sabuwar gwamnatin da zai nada musamman sabuwar ranar Demokradiyya 12 ga Yuni. Ana kyautta zaton cewa nan da ranar 29 ga Mayu, wasu sunayen zasu fara bayyana.

Majiyar Aljazirah ta bayyana cewa shugaba Muhammadu Buhari na shirin nada tsohon gwamnan jihar Legas a zamanin mulkin soja, Janar Buba Marwa ko kuma tsohon shugaban hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zabon kasa wato EFCC, Nuhu Ribadu.

Daya daga cikinsu zai maye kujerar Abba Kyari, mai ci a yanzu.

Abinda ya sa Buhari ke tunanin nada Buba Marwa ko Nuhu Ribadu shine a wannan karon, yana bukatar kwararre ko kuma wanda ya taba aikin soja.

Aljazirah Nigeria, ta tattaro cewa Buba Marwa ne yafi cancanta bisa ga bukatun Buhari fiye da kowa amma tarihin Nuhu Ribadu kan yaki da cin hanci da rashawa ka iya sa Buhari ya nada shi.

Wata majiyar daban ta bayyana cewa wandannan mutane guda biyu ko ta kaka suna cikin mutane biyar da shugaba Buhari zai fara nadawa a sabbin nade-nadensa guda biyar.

Nade-naden sune shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, babban mai baiwa shugaban kasa shawara kan tsaro NSA, sakataren gwamnatin tarayya, shugaban ma'aikatan gwamnati, da mai magana da yawun shugaban kasa.

Sauran wadanda ka iya samun shiga sune Dame Pauline Tallen, Gwamna Jibrilla Bindow, Adamawa, Gwamna Mohammed Abubakar, Bauchi, Hon Ahmed Aliyu Wadada, Nasarawa, da Hon Emmanuel Jime, Benue.

Majiya yta bayyana cewa an tattara wadannan sunaye ne lokacin da shugaban kasan a kai ziyara kasar Ingila.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel