Zaben gwamnan Kano: Ganduje zai gabatar wa kotu kundi mai shafi 1,800

Zaben gwamnan Kano: Ganduje zai gabatar wa kotu kundi mai shafi 1,800

Wani babban lauya kuma lauyan Abdullahi Umar Ganduje a kotun sauraron karan zabe da ke zama a Miller Road, Bompai, Kano ya bayyana cewa Ganduje ya shirya kundi mai dauke da shafi 1,800 kuma a shirye yake ya gabatar da shaidu 203 tare da su.

“Mun shirya don nuna ma duniya cewa tabbas an gudanar da zabe na gaskiya da adalci a ranar 23 ga watan Maris, 2019”, cewar lauyan shi Barista Musa Abdullahi Lawan.

Yayin da yake magana bayan ya shirya takardun gwamnan a gaban kotun sauraran karan, Barista MA Lawan, wanda ya kasance daya daga cikin jagoran lauyoyin gwamnan, yace ikirarin da jam’iyyar PDP ta gabatar gaban kotun ba mai inganci bane.

Zaben gwamnan Kano: Ganduje zai gabatar wa kotu kundi mai shafi 1,800

Zaben gwamnan Kano: Ganduje zai gabatar wa kotu kundi mai shafi 1,800
Source: Twitter

Barista MA Lawan yace zasu gabatar da shaidu 203 wadanda suka kasance masu muhimmanci, zasu kuma fada ma kotun cewa tabbas an gudanar da zabe da kuma cewa jam’iyyar PDP ta gabatar da kara mara tushe.

KU KRANTA KUMA: Dalilin da yasa aka haramta yin tashe a Kano

Lauyan Gandujen yayi watsi da rade-radin cewa jihar ta tayi amfani da damar yima alkalai sauyin wjen aiki domin shigo da wadanda zasu goya musu baya. Ya kuma dage cewa akwai kararraki 50 a gaban kotun kuma yawancinsu sunyi ma kotun yawa.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel