Kakakin Majalisar Wakilai: Buhari na goyon bayan Kudu maso Gabas

Kakakin Majalisar Wakilai: Buhari na goyon bayan Kudu maso Gabas

A yayin da ake gab da shiga lokaci na samar da shugabannin majalisun tarayya a tsakanin jam'iyya mai ci ta APC da kuma jam'iyyar adawa ta PDP, 'yan siyasa da dama na ci gaba kai ruwa rana domin cimma manufofin su.

Wani tsohon kakakin majalisar dokoki na jihar Imo, Mista Amaechi Nwoha, na ci gaba da kyautata zato a kan cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari zai shimfida goyon bayan sa wajen kebance kujerar kakakin makalisar wakilai zuwa ga dan kabilar Ibo.

Kakakin Majalisar Wakilai: Buhari na goyon bayan Kudu maso Gabas

Kakakin Majalisar Wakilai: Buhari na goyon bayan Kudu maso Gabas
Source: Depositphotos

Yayin shaidawa manema labarai na kasa a ranar Asabar cikin garin Abuja, Nwoha ya ce shugaban kasa Buhari ya kasance adalin jagora da ya tsarkaka daga duk wani nau'i na kabilanci a yayin da ya riki dukannin al'ummar kasar nan sa matsayin daya.

Nwoha ya misalta shugaba Buhari a matsayin Uba ga dukkanin al'ummar Najeriya wanda gwamnatin sa ta tsarkaka daga nuna wariya ga kowane yanki tare da jajircewa wajen tabbatuwar kasar nan tamkar tsintsiya madauri guda.

KARANTA KUMA: Masu garkuwa da Mutane sun kashe Lakcara a Najeriya

Da yake neman sauran jiga jigan jam'iyyar APC wajen riko da adalci, Nwoha ya kuma nemi shugaban kasa Buhari wajen goyon bayan kebance kujerar kakakin majalisar wakilai zuwa ga yankin Kudu maso Gabashin Najeriya.

Domin tabbatuwar burin gwamnatin Buhari wajen hada kawunan al'ummar kasar nan wuri guda, Nwoha ya ce samar da kakakin majalisar wakilai dan kabilar Ibo zai yi tasirin gaske wajen karfafa mashahuranci da kuma nasabar jam'iyyar APC a yankin Kudu maso Gabas.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta a Facebook ko kuma Twitter:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi:

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel