Gwamnonin PDP sun yi warsi da El-Rufai a tseren mutum 2 da ke neman shugabancin kungiyar gwamnonin Najeriya

Gwamnonin PDP sun yi warsi da El-Rufai a tseren mutum 2 da ke neman shugabancin kungiyar gwamnonin Najeriya

Gabannin zaben shugaban kungiyar gwmnonin Najeriya, akwai alamu dake nuna cewa gwamnonin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) sun fi son takwaransu na jihar Ekiti, Dr. Kayode Fayemi bisa gwamnan jihar Kaduna Nasir el-Rufai.

Kungiyar NGF karo na bakwai zata gudanar da zabenta a ranar Laraba a Abuja.

El-Rufai na iya ja baya a takaran bayan tattaunawa tsakanin gwamnonin All Progressives Congress (APC), jaridar The Nation ta ruwaito.

Kungiyar gwamnonin ta samar da shuwagabanni shida a cikin shekaru 20 da suka gabata a damukardiyyan kasar.

Gwamnonin PDP sun yi warsi da El-Rufai a tseren mutum 2 da ke neman shugabancin kungiyar gwamnonin Najeriya

Gwamnonin PDP sun yi warsi da El-Rufai a tseren mutum 2 da ke neman shugabancin kungiyar gwamnonin Najeriya
Source: UGC

Shugabannin sun hada da: Alh. Abdullahi Adamu, (Nasarawa, 1999 – 2004), Arc. (Obong) Victor Attah (jihar Akwa Ibom , 2004 -2006), Chief Lucky Igbinedion (Edo, 2006 – 2007), Dr. Abubakar Bukola Saraki (Kwara, 2007- 2011), Rotimi Amaechi (Rivers, 2011 -2015) da kuma Abdulaziz Yari (2015-2019).

Yankin kudu maso yamma, yankin arewa maso gabas, da kuma yankin kudu maso gabas basu samu shugabancin kungiyar ba tukun.

An tattaro cewa hankalin yawancin gwamnonin PDP bai kwanta da El-rufai ba saboda yanayin da ya dauki jam’iyyar adawa da kuma ra’ayoyinsa masu tsauri akan wassu lamuran da suka shafi kasa, musamman ta fannin addini.

KU KARANTA KUMA: Babu wanda ya isa ya hana a rantsar da ni - Tambuwal

Wasu gwamnonin PDP na kallon El-rufai a matsayin babban wanda yayi sanadiyar kayar da jam’iyyar adawa a zaben kasa da ya gabata.

Gwamnonin zasu halarci taron tattalin arziki karo na karshe a ranar Laraba. Zasu yi amfani da daman wajen zaban sabon shugaba.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel