Masu garkuwa da Mutane sun kashe Lakcara a Najeriya

Masu garkuwa da Mutane sun kashe Lakcara a Najeriya

Kamar yadda muka samu, jaridar Premium Times ta tabbatar da cewa mummunan ta'addancin masu garkuwa da mutane ya hallaka wani Lakcara na jami'ar Igbinedion da ke garin Okada a jihar Edo, Kelvin Izevbekhai.

Hukumar jami'ar Igbinedion da kuma kwamshinan 'yan sanda na jihar Edo, Muhammad Dan Mallam, a ranar Lahadin da ta gabata sun yi tarayya wajen bayar da shaida ta aukuwar wannan mummunar ta'ada.

Masu garkuwa da Mutane sun kashe Lakcara a Najeriya

Masu garkuwa da Mutane sun kashe Lakcara a Najeriya
Source: Facebook

Dan Mallam ya ce Mista Kelvin ya riga mu gidan gaskiya ta hanyar harbi na harsashin bindiga yayin yunkurin sa na tserewa daga hannun masu garkuwa da mutane bayan sun kada keyar sa tare da sauran wadanda azal ta afka kan su cikin dokar daji.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito cewa, masu garkuwa da mutane rike da makamai na bindigu sun ci karen su babu babbaka wajen datse matafiya a hanyar garin Okada daura da babbar hanyar Benin zuwa Legas.

KARANTA KUMA: Dangote ya hau mataki na 11 cikin jerin manyan jagorori hamsin masu tasiri a duniya

Mista Jide lugbo, kakakin jami'ar Igbinedion yayn bayyana bakin cikin sa a kan aukuwar wannan mummunar ta'asa, ya hikaito yadda marigayi Kelvin a shekarar 2016 ya samu aikin koyar wa a jami'ar bayan ya kasance dalibin ta a sakamakon hazakar sa.

Legit.ng ta fahimci cewa, ta'addancin garkuwa da mutane tare da neman kudin fansa ya yi kamari a sassan Najeriya da dama ka ma daga yankunan jihohin Ondo, Katsina, Kaduna da kuma Zamfara.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta a Facebook ko kuma Twitter:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi:

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel