Babu wanda ya isa ya hana a rantsar da ni - Tambuwal

Babu wanda ya isa ya hana a rantsar da ni - Tambuwal

- Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal, yayi zargin cewa wasu na shirye shiryen haddasa rigingimun siyasa a jihar

- Tambuwal ya jaddada cewa babu wanda ya isa ya hana a rantsar da shi a ranar 29 ga watan Mayu

- Gwamnan ya karfafa cewa kotu kadai ce take da karfin hana gwamnatinsa

Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal, a jiya Lahadi, 19 ga watan Mayu yayi zargin shirye shiryen haddasa rigingimun siyasa a jihar, kamar yanda ya jaddada cewa babu wanda ya isa ya hana a rantsar da shi a ranar 29 ga watan Mayu.

Yayin da yake magana ta hannun babban hadiminsa, Alhaji Yusuf Dingyadi, gwamnan yayi zargin cewa wassu mutane suna yada karerayi da kuma haddasa rudani cewa kotu tana shirin tsige shi daga kujerarsa sannan ta mika mulkin ga APC.

Babu wanda ya isa ya hana a rantsar da ni - Tambuwal

Babu wanda ya isa ya hana a rantsar da ni - Tambuwal
Source: Twitter

Ya kara da cewa an cire fostan shi da aka lika a hanyar Birnin Kebbi, hanyar tashar jirgi da Maiduguri an kuma mayar da fostan dan takaran jam’iyyar APC.

Tambuwal ya karfafa cewa kotu kadai ce take da karfin hana gwamnatinsa.

KU KARANTA KUMA: Dalilin da yasa aka haramta yin tashe a Kano

Gwamnan ya shawarci jam’iyyar adawa da ta “bar kotu ta gudanar da aikin ta, jam’iyyar PDP a Sokoto bata nemi hukunci ta kofar baya ba. Kawai a bar kotu tayi abunda ya dace, muna da tabbaci akan kotu saboda mun lashe zabe ne da ikon Allah.”

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel