Dangote ya hau mataki na 11 cikin jerin manyan jagorori 50 masu tasiri a duniya

Dangote ya hau mataki na 11 cikin jerin manyan jagorori 50 masu tasiri a duniya

An kiyasta cewa fitaccen attajirin nan da ya yiwa duk wani Mahaluki zarra da fintinkau ta fuskar dukumar dukiya da tarin arziki a nahiyyar Afirka, Aliko Dangote, shi ne a mataki na 11 cikin jerin manyan jagorori hamsin masu tasiri a duniya a bana.

Mujallar Fortune ta kasar Amurka dake gudanar da kiyasi akan harkokin da suka shafi kasuwanci, ita ta fidda kididdigar wannan sakamako a kwana kwanan nan kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Aliko Dangote

Aliko Dangote
Source: Getty Images

Kamar yadda maruwaita suka bayar da shaida, mujallar Fortune ta shahara wajen gudanar da kididdiga da kuma kiyasa akan manyan 'yan kasuwa na duniya dake da fifikon tasiri a fagen inganta rayuwar al'umma.

Mujallar ta yi bayanin cewa, manyan jagorori na duniya da suka hadar da Mata da kuma Maza na ci gaba da bayar da mafificiyar gudunmuwa wajen kawo muhimmin sauyi a fadin duniya ta hanyar inganta jin dadin rayuwar al'umma da kuma kasancewar su abin koyi a fannin al'amurran da suka shafi kasuwanci, gwamnati, fasaha da kuma jin kai.

KARANTA KUMA: Kada ka bari sabanin ka da Buhari ya mayar da kai sakarai - Sule Lamido ya yiwa Obasanjo raddi

Legit.ng ta fahimci cewa, wannan shi ne karo na farko da kididdigar mujallar Fortune da gano muhimmanci Dangote tare da sanya shi cikin sahun manyan jagorori na duniya masu tasiri a kiyasin ta na bana.

Jerin manyan jagorori goma masu tasiri a fagen inganta jin dadin rayuwar al'umma kamar yadda mujallar Fortune ta kiyasta sun hadar:

1. Bill Gates (Bill & Melinda Gates)

2. Jacinda Ardem (Firai Ministar kasar Zealand)

3. Robert Mueller

4. Pony Ma (Tencent)

5. Satya Nadelle (Microsoft)

6. Greta Thunberg

7. Margrethe Vestager

8. Anna Nimiriano

9. Jose Andres

10. Dough Mcmllon & Lisa Woods

Dangote ya hau mataki na goma sha daya a sakamakon gagarumar gudunmuwar da yake bayar wa ta hanyar amfani da gidauniyar sa ta Dangote Foundation wajen yakar cutar shan inna da sauran al'amurra da suka shafi jin kai na kiwon lafiyar al'umma.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta a Facebook ko kuma Twitter:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi:

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel