Tattalin arziki: Hannun jari za su yi kasuwa a Najeriya inji Kwararru

Tattalin arziki: Hannun jari za su yi kasuwa a Najeriya inji Kwararru

Mun samu labari Masana harkar kasuwar hannun jari sun bayyana cewa ana sa rai kasuwa ta mike bayan an sake rantsar da shugaban kasa Muhammadu Buhari a Ranar 29 ga Watan Mayun nan.

Wadanda su ka laƙanci sirrin kasuwar hannun jari sun ce darajar hannun jari zai dawo da karfinsa da zarar shugaba Buhari ya koma kan karagar mulki a karo na biyu, sannan ya kuma kafa gwamnati.

Masu bincike sun ce kasuwar hannun jarin Najeriya zai rikiɗe da zarar an tabbatar da sabon gwamnati a kasar, musamman idan aka naɗa Ministocin da ke da sha’awar harkar kasuwanci.

Wadannan masu bincike a kamfanin Cowries Research sun ce abin da zai iya kawowa kasuwar hannun jari cikas a Najeriya shi ne shari’ar da ake yi a kan zaben 2019 tsakanin APC da kuma PDP.

KU KARANTA: Buhari ya karbe wani babban kwangila daga hannun kamfanin Atiku

Masanan sun ce rashin sanin yadda shari’ar zaben na bana za ta kaya na iya jawa masu hannun jari su guji shigowa Najeriya domin kuwa babu wanda ya san halin siyasar da kasar za ta kare a ciki.

Alkaluman da aka fitar kwanan nan sun nuna cewa an samu karancin masu zuba hannun jari a Najeriya a farkon shekarar nan, idan aka kamanta da abin da aka rika samu a karshen shekarar bara.

Daily Trust tace an samu hakan ne a dalilin harkar zabe da aka yi da kuma tsare-tsaren CBN da su ka gaza kai tattalin arzikin kasar ga ci, sannan kuma da alhakin wani sabon shirin fansho na kasar.

Ana sa rai dai da zarar shugaba Buhari ya koma kan mulki yayi maza ya fitar da jerin Ministoci da sauran wadanda zai yi aiki da su domin a san alkiblar da gwamnatin sa ta dosa tun da wuri.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel