Matashi ya fille kan abokinsa ya kai ma boka don ayi masa kudin tsafi

Matashi ya fille kan abokinsa ya kai ma boka don ayi masa kudin tsafi

Wani matashi mai suna Samuel ya kashe abokinsa mai suna Muhammad Saba ta hanyar fille masa kai da nufin kai ma wani boka don yayi masa hanyar samun arziki ta aiki da aljanu da tsubbace tsubbace, inji rahoton Daily Trust.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito a ranar 4 ga watan Mayu ne Yansanda suka kama Samuel da abokansa ne a daidai garin Lambata dake kan hanyar Suleja zuwa Minna yayin da yake tuka motar Muhammad kirar Toyota Camry mai lamba ABC 314 KJ.

KU KARANTA: Yan bindiga sun kai hari cocin Kaduna, sun yi garkuwa da Fasto da yan mata 10

Rahotanni sun bayyana cewa yayin da yan bindigan suka hangi Yansanda sai suka bude musu wuta, daga nan suma Yansandan suka mayar da biki, a sanadiyyar haka suka dirka ma Samuel harsashi a kafarsa.

Kaakakin rundunar Yansandan jahar, DSP Muhammad Dan-Inna Abubakar ya bayyana cewa bayan Yansanda sun ci karfinsu, sai suka kaddamar da binciken kwakwaf akan motar, anan suka ci karo da kan gutulallen kan Muhammad a cikin motar.

Yayin da yaji matsa, sai Samuel ya bayyana ma Yansanda gaskiya, inda yace a jahar Nassarawa ya kashe Muhammad, daga nan ya jefar da gangan jikinsa sa’annan yayi awon gaba da motarsa, ya kara da cewa Muhammad dan asalin garin Tsaragi ne.

Sai dai shima Samuel ya rigamu gidan gaskiya sakamakon zubar da jini da yayi dayawa daga raunin daya samu a kafarsa, inda ya mutu a yayin da aka garzaya dashi Asibiti, kuma likitoci suka tabbatar da mutuwar tasa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel