Gungun yan bindiga sun bude masu kallon kwallo wuta a garin Jos

Gungun yan bindiga sun bude masu kallon kwallo wuta a garin Jos

Akalla mutum guda ne ya rigamu gidan gaskiya, yayin da wasu da dama suka samu munana raunuka sakamakon wani mummunan hari da wasu yan bindiga suka kai a wani gidan kallon kwallo dake garin Jos na jahar Filato.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito wannan lamari ya auku ne a ranar Asabar, yayin da ake buga kwallon wasan karshe na kofin FA na kasar Ingila tsakanin kungiyar Manchester City da Watford, inda Manchester ta lallasa Watford 6-0.

KU KARANTA: Mun amince da umarnin Buhari na sakar ma kananan hukumomi mara su yi fitsari – Gwamnoni

Shaidun gani da ido sun bayyahna cewa yan bindigan da ake zargin matasan wata kungiyar asiri ne sun kutsa kai cikin sashin kallon kwallo ne na Otal din Garden Palace and Bar dake unguwar Busa Buji na garin Jos da misalin karfe 7 na yamma, suka bude ma yan kallo wuta.

Wani daya tsallake rijiya da baya mai suna Phillips ya bayyana cewa yan bindigan sun kashe wani matashi mai suna John Davou a gabansa sakamakon harbin da suka yi masa sau uku akai, sa’annan sun kasne wani matashi a gabansa.

Shima ma shaidan gani da ido, Mathew yace “Ina tunanin John Davou suka je nema, domin shi kadaine ya sha ruwan alburusai, yayin da sauran jama’a suka samu rauni daga harbe harben da suka yi. A kwanakin nan John ya zana jarabawar JAMB da nufin shiga jami’a, gaskiya basu kyauta masa ba.”

Sai dai duk kokarin da majiyarmu tayi na jin ta bakin kaakakin rundunar Yansandan jahar, Terna Tyopev yaci tura sakamakon duk layukan wayoyinsa a kashe suke.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel