Yan bindiga sun kai hari cocin Kaduna, sun yi garkuwa da Fasto da yan mata 10

Yan bindiga sun kai hari cocin Kaduna, sun yi garkuwa da Fasto da yan mata 10

Wasu gungun yan bindiga sun kai farmaki akan wani coci dake karamar hukumar Birnin Gwari ta jahar Kaduna inda suka yi awon gaba da mata goma yan kungiyar wake waken cocin, da kuma masu bauta guda bakwai inji jaridar Kaakaki Reporters.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito wannan lamari ya faru ne a ranar Asabar, 18 ga watan Mayu yayin da yan kiristoci ke gudanar da bauta a cocin Evangelical Church Winning All, ECWA, dake kauyen Dankande cikin karamar hukumar Birnin Gwari, sai dai har yanzu ba’a san halin da Faston cocin yake ciki ba.

KU KARANTA: Mun amince da umarnin Buhari na sakar ma kananan hukumomi mara su yi fitsari – Gwamnoni

Da yake tabbatar da aukuwan lamarin, shugaban kungiyar kiristocin Najeriya, CAN, reshen karamar hukumar Birnin Gwari, Fasto Emmanuel Ibrahim ya bayyana cewa yan bindigan sun kai samame cocin ne da yammacin ranar Asabar.

“Isarsu keda wuya suka amshe wayoyon dukkanin wadanda suka tarar a cocin, sa’annan suka tambayesu ina Faston cocin, cikin halin razana da tsoro yan matan suka nuna gidan Faston, daga nan suka yi awon gaba dashi, diyarsa da sauran mutane goma sha biyar.” Inji shi.

Da majiyarmu ta tuntunbi kaakakin rundunar Yansandan jahar Kaduna, DSP Uakubu Sabo don jin ta bakinsa, sai yace bashi da wannan labari, amma zai tambaya ya dawo mata da amsa, amma shiru kake ji har zuwa lokacin tattara wannan rahoto.

A wani labarin kuma wasu gungun yan bindigan sun kaddamar da mummunan hari a wani cocin Nasara Baptis dage kauyen Guguwa kusa da garin Rigasa dake cikin karamar hukumar Igabi ta jahar Kaduna, inda suka kashe wani mutumi Obadiah Samson tare da yin garkuwa da masu bauta guda biyu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel