Sanata Gbemisola Saraki tana hangen kujerar Ministan Tarayya a 2019

Sanata Gbemisola Saraki tana hangen kujerar Ministan Tarayya a 2019

Labari ya fara zuwa mana cewa an fara shirin fafatawa a game da wanda zai zama Ministan gwamnatin tarayya daga jihar Kwara inda manyan ‘yan siyasan da ake ji da su a jihar su ka kunno-kai.

A halin yanzu Magoya-bayan Sanata Gbemisola Saraki sun budo wuta, yayin da Masoyan Alhaji Lai Mohammed a wani bangaren, su ke ganin da su za a sake komawa gwamnatin shugaba Buhari.

Gbemisola Saraki, ‘Diya ce wajen babban ‘Dan siyasar da aka yi a Kwara watau Marigayi Sanata Olusola Saraki. Shi kuma Lai Mohammed yana cikin manyan tafiyar APC tun a lokacin kafuwarta.

Kowane cikin Gbemi Saraki da Lai Mohammed yana sa rai shugaba Buhari ya ba sa kujerar Minista a dalilin irin kokarin da su ke gani sun yi wa jam’iyyar a zaben bana wajen rusa jam’iyyar PDP.

KU KARANTA: Atiku na kokarin hana Gwamnatin Buhari motsi – Lai Mohammed

Sanata Gbemisola Saraki tana hangen kujerar Ministan Tarayya a 2019

Magoya bayan Gbemisola Saraki su na so a ba ta Minista

Saraki tana cikin wadanda su ka nakasa jam’iyyar PDP ta ‘Danuwan ta watau Bukola Saraki a jihar Kwara a zaben 2019, kuma tsohuwar Sanatan tana tare da wasu manyan kusoshi na jam’iyyar APC.

Shi kuma Lai Mohammed wanda tsohon Kakakin APC ne, yana tare ne da Asiwaju Bola Tinubu. Lai yayi aiki da Tinubu a lokacin yana gwamnan jihar Legas kafin ya nemi takarar gwamna a Kwara a 2003.

Yanzu dai za a zura idanu a ga wanda Buhari zai dauko a matsayin Ministansa daga jihar ta Kwara. Lai Mohammed dai ya dade a cikin APC yayin da Gbemi Saraki ta bar PDP ne daf da zaben 2015.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Tags:
Online view pixel