Bola Tinubu: Salvador yayi kaca-kaca da Gwamnan Kaduna El-Rufai

Bola Tinubu: Salvador yayi kaca-kaca da Gwamnan Kaduna El-Rufai

Daily Trust ta rahoto cewa wani daga cikin manyan Jagororin jam’iyyar APC a jihar Legas, Moshood Salvador, ya fito ya jinjinawa babban jigon jam’iyyar watau Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.

Moshood Salvador yake cewa Mutanen Kudu maso Yamma da ma Najeriya gaba-daya sun yi dace da samun irin Bola Tinubu. Salvador ya fadawa manema labarai wannan ne wajen wani taron tafsiri.

Salvador yake cewa babu wanda ya isa yayi maganar irin cigaban da Legas da ta samu daga 1999 zuwa yau, ba tare da kawo sunan tsohon gwamna Tinubu ba inda ya soki kalaman gwamna Nasir El-Rufai.

Babban ‘Dan siyasar yake cewa babu dalilin maganganun da El-Rufai yayi na cewa siyasar Uban-gida ya hana jihar Legas cigaba. Salvador yace mutanen Legas ba su taba kokowa a kan Bola Tinubu ba.

KU KARANTA: APC ta kare El-Rufai a kan zargin sukar Jigon Jam'iyya Tinubu

Bola Tinubu: Salvador yayi kaca-kaca da Gwamnan Kaduna El-Rufai

Salvador yace Tinubu yayi aikin da ya shiga tarihi a Legas
Source: Depositphotos

Tsohon shugaban jam’iyyar PDP yake cewa duk da gwamnan na Kaduna bai kama suna ba, jawabinsa ya nuna cewa da Bola Tinubu yake domin shi ne babban jigon jam’iyyar APC a jihar Legas.

“Akwai bukatar Gwamnan Kaduna ya fahamci cewa bai dace ya tattara ya zo har Legas yana jawabi a kan siyasar Uban-gida ba”

Ya kuma kara da cewa

“Ba mu da wata matsala da manyan Jagororin siyasar mu da ke Legas don haka El-Rufai ya ji da harkokin gabansa, ya raba kansa da zuwa Legas yana fadin abin da ba a tambaye sa ba”

Mista Salvador yake cewa ya kamata gwamna Nasir El-Rufai ya koma gidansa ne yayi maganin matsalar tsaro da rashin albashi da kashe-kashen da ake yi ba ya rika tsoma baki a cikin siyasar Legas ba.

“Mu na samun labarin matsalolin da ake fama da su a Kaduna: na rashin albashi da kashe-kashen Bayin Allah. El-Rufai bai yi maganin wadannan abubuwa ba, amma yana tsoma baki a cikin harkar Jiha irin Legas da abubuwa su ke tafiya daidai”

A jawabin na sa na Ranar Lahadin nan, 19 ga Watan Mayu, Salvador yace ba za su bari a rika taba Tinubu ba domin kuwa babu wanda su ke ji da shi a tarihin siyasa da ya fi sa illa marigayi Obafemi Awolowo.

“Ba za mu bari a cigaba da cin mutuncin Bola Tinubu ba, saboda irin kokarin da yayi a Legas daga 1999. Ba zai yiwu a ambaci Legas ba tare da a kira sunan Tinubu. A kasar Yarbawa babu wanda ya sha gabansa sai Awolowo, don haka ba za a rika sukar sa mu kyale ba.”

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel