Buhari ya sha ruwa tare da Abulaziz Yari a Saudiyya, ya yi magana a kan kisan Zamfara

Buhari ya sha ruwa tare da Abulaziz Yari a Saudiyya, ya yi magana a kan kisan Zamfara

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sha ruwa tare da gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Yari, tare da sarkin Maradun, Alhaji Garba Tambari, ranar Lahadi a kasar Saudiyya.

Kakakin shugaban kasa, Garba Shehu, ne ya bayyana a cikin wani jawabi da ya fitar a Abuja.

Yayin shan ruwan bayan an kai azumin watan Ramadana, shugaban Buhari ya bayyana bacin ran sa da kisan rayukan jama'a da lalata dukiya da sakamakon hare-haren 'yan bindiga a jihar Zamfara.

Kakakin na shugaban kasa ya rawaito cewar shugaba Buhari ya furta cewa; "za mu tabbatar da adalci domin ganin cewar dukkan 'yan Najeriya sun samu kwanciyar hankali da cigaba a duk inda suka samu kan su."

Buhari ya sha ruwa tare da Abulaziz Yari a Saudiyya, ya yi magana a kan kisan Zamfara

Buhari a Saudiyya
Source: Twitter

Sarkin Muradun ya jagoranci addu'o'i na musamman ga wadanda suka rasa rayukan su sakamakon aiyukan 'yan ta'adda a jihar Zamfara da ma fadin Najeriya tare da yin addu'ar Allah ya bawa Najeriya zama lafiya da yalwar arziki.

DUBA WANNAN: 'Yan bindiga sun sace mutane 8 a Zamfara, sun nemi N50m

Shehu ya bayyana cewar shugaba Buhari ya samu zuwa wurin shan rakiyar bisa rakiyar jakadan Najeriya a kasar Saudiyya, Jastis Isa Dodo (mai ritaya).

Watan azumin Ramadana lokaci ne na yin ibada da rokon yafiya da samun kwanciyar hankali da gudanar da addu'o'i na musamman.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel