Kada ka bari sabanin ka da Buhari ya mayar da kai sakarai - Sule Lamido ya yiwa Obasanjo raddi

Kada ka bari sabanin ka da Buhari ya mayar da kai sakarai - Sule Lamido ya yiwa Obasanjo raddi

- Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido, ya kirayi tsohon shugaban kasar Najeriya Olusegun Obasanjo, da ya janye kalaman sa da bayyana akan manufar ta'addancin Boko Haram

- Obasanjo ya yi ikirarin cewa ta'addancin Boko Haram manufa ce ta Musuluntar da yankin Afirka ta Yamma

- Tsohon gwamna Lamido ya ce kada sabanin akida tsakanin Obasanjo da gwamnatin Buhari ya mayar da shi sakarai

Tsohon gwamnan jihar Jigawa Alhaji Sule Lamido, ya shawarci tsohon shugaban kasar Najeriya, Cif Olusegun Obasanjo, a kan cewa kada sabanin sa da gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta mayar da shi sakarai.

Sule Lamido tare tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo raddi

Sule Lamido tare tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo raddi
Source: UGC

Cikin wata sanarwa a ranar Lahadi, 19 ga watan Mayun 2019, Lamido wanda ya kasance tsohon Ministan harkokin kasashen ketare a gwamnatin tsohon shugaban kasa, ya nemi Obasanjo da ya dawo daga rakiyar furucin sa na cewar ta'addancin Boko Haram wata babbar manufa ce ta yunkurin musuluntar da yankin Afirka ta Yamma.

Tsohon shugaban kasa cikin kalaman sa kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito ya bayyana cewa, a halin yanzu babu wani batu na rashin ilimi, rashin aiki ko kuma katutu na talauci a tsakanin matasa da yake ci gaba da rura wutar ta'addanci a Najeriya face miyagun ababe dake aukuwa da manufa ta musuluntar da nahiyyar Afirka baki daya.

Kamar yadda majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito, tsohon shugaban kasar ya bayyana hakan cikin jawaban da ya gabatar yayin halartar babban taron hudubar mabiya mazhabar Anglican na addinin Kirista a karamar hukumar Isoko ta Kudu da ke jihar Delta a ranar Asabar.

KARANTA KUMA: Mutane 6 da suka fi kowa girman hannun jari a kamfanin sadarwa na MTN

A yayin shimfida yakinin sa da cewar kungiyar masu tayar kayar baya ta Boko Haram ta sha gaban gwamnati ta fuskar karfi a sakamakon hadin gwiwar ta da mafi munin kungiyar ta'adda ta ISIS, tsohon shugaban kasa Obasanjo ya ce gwamnatin Najeriya ba ta biyo hanyar da ta dace ba wajen magance ta'addancin Boko Haram tun fil azal.

Da ya ke babatu cikin wata sanarwa da sanadin mai magana da yawun sa, Mansur Ahmed, tsohon gwamnan na jihar Jigawa ya ce ko kusa Obasanjo bai dace da furucin sa ba musamman yadda ya gabatar da shi a wurin taro na ibada.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta a Facebook ko kuma Twitter:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi:

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel