Lauyoyin Atiku sun rubuta takarda na shirin kai Lauretta Onochie a Kotu

Lauyoyin Atiku sun rubuta takarda na shirin kai Lauretta Onochie a Kotu

Mun ji labari cewa ‘Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar adawa ta PDP a zaben bana, Atiku Abubakar, yayi barazanar kai karar wata daga cikin Hadiman shugaba Muhammadu Buhari kara a gaban kotu.

Atiku Abubakar ya nemi Lauretta Onochie ta janye wasu kalamai da tayi a kafafen yada labarai kwanakin baya. Tsohon mataimakin shugaban kasar yayi kira ga Onochie ta dawo daga rakiyar wani zargi da ke yi a kan sa.

Atiku ya rubutawa Lauretta Onochie wasika ta bakin Lauyoyinsa a Ranar 14 ga wannan Watan na Mayu kamar yadda mu ka samu labari. Onochie ta yada wani labari da tace an sa Atiku cikin wadanda ake nama ido-rufe a kasar UAE.

KU KARANTA:

Lauyoyin Atiku sun rubuta takarda na shirin kai Lauretta Onochie a Kotu

Atiku yana so Lauretta Onochie ta biya sa Miliyan 500 na bata masa suna
Source: UGC

Onnochie take cewa Atiku ya kan yi safarar ‘yan ta’adda a Dubai a lokacin da ya je kasar kwanaki. Rahoton ya nuna cewa Alhaji Atiku Abubakar zai maka Mai ba shugaban kasar shawara idan ba ta janye wannan kalaman da tayi ba.

Lauyan da ke kare babban ‘dan siyasar, Mike Ozekhome, yake cewa maganganun Onochie sun jawo Atiku Abubakar ya shiga cikin wani yanayi na babu dadi. Amma har yanzu dai Onochie ba ta da alamar goge wannan jawabi da tayi.

Ozekhome ya ba Hadimar shugaban kasar sa’a 48 ta dauke bayanin da tayi a Tuwita. Lauyan ya kuma nemi Mai ba shugaban kasar shawara ta biya Atiku kudi Miliyan 500 na bata masa suna ko ayi mata ukuba idan ta gaza yin haka.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel