Kasar Indonesia za ta koro matar El-Rufa'i da dan sa gida

Kasar Indonesia za ta koro matar El-Rufa'i da dan sa gida

Asiya El-Rufa'i, daya daga cikin matan gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa'i, tare da dan ta na fuskantar barazanar dawo da su gida Najeriya daga kasar Indonesia.

Asiya 'yar uwa ce ga fitacciyar 'yar jarida kuma 'yar gwagwarmaya, Kadaria Ahmed.

SaharaReporters ta wallafa cewar majiyar ta, ta sanar da ita cewar duk da Asiya na da bizar shiga kasar, amma ta na fuskantar matsala saboda rashin wata takarda.

Jaridar ta kara da cewa majiyarta ta sanar da ita cewar gwamnatin Najeriya ta shiga tsakani domin warware matsalar da iyalin gwamnan ke fuskanta a kasar Indonesia.

"Yanzu haka gwamnatin Najeriya ta shiga maganar kuma su na kokarin warware matsalar da gwamnatin kasar Indonesia," a cewar majiyar.

Kasar Indonesia za ta koro matar El-Rufa'i da dan sa gida

El-Rufa'i da matar sa Asiya
Source: Twitter

Sai dai ba a bayyana me ya kai Asiya tare da dan ta kasar Indonesia ba. Kazalika babu wani jawabi daga gwamnatin jihar Kaduna ko ofishin El-Rufa'i a kan abinda ya kai iyalin gwamnan kasar Indonesia ko kuma karin bayani a kan matsalar da suke fuskanta.

DUBA WANNAN: Gaskiyar abinda yasa Ganduje ke yakar sarki Sanusi II

Ba bakon abu bane a wurin masu mulki, musamman masu rike da mukaman siyasa, a Najeriya su fita kasashen ketare tare da iyalinsu domin yawon bude ido ko duba lafiyar su.

Ba kasafai yaran irin wadannan mutane ke zama a Najeriya domin halartar makarantu ba.

Irin wannan hali na shugabannin mu ne yasa ragowar kasashen duniya ke yiwa Najeriya kallon kaskanci da raini da kuma nuna shakku a kan niyya da ikirarin shugabannin kasar mu na kawo gyara a harkokin kasar, musamman bangaren kiwon lafiya da inganta ililmi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel