Tudun Wus: Sama da mutane 1,000 ke fuskantar matsin rayuwa saboda karancin ruwa

Tudun Wus: Sama da mutane 1,000 ke fuskantar matsin rayuwa saboda karancin ruwa

- Al'ummar garin Tudun Wus a jihar Bauchi, sun koka kan matsanancin rashin ruwa da suke fama da shi tsawon shekaru

- Shugaban gargajiya na garin, Jibrin ya ce garin na da fanfunan tuka-tuka guda tara, amma gaba dayansu sun daina aiki kusan shekara daya baya

- Sai dai, hukumar samar da ruwa tare da tsaftace shi a kauyuka da karkara (RUWASSA), ta jaddada cewa ba ta karbi wani korafi daga al'ummar ba har yanzu

Al'ummar garin Tudun Wus, karamar hukumar Dass da ke a jihar Bauchi, sun yi kira ga gwamnatin jihar da ta tarayya, kungiyoyi masu zaman kansu, da ma masu hannu da shuni, da su ceci garin daga matsanancin rashin ruwa da suke fama da shi tsawon shekaru.

Shugaban gargajiya na garin, Malam Babaji Jibrin, ya yi wannan kiran a lokacin da wakilan Legit.ng TV Hausa suka kai ziyara a garin domin ganewa idanuwansu halin da al'ummar garin ke ciki na rashin ruwa, yana mai cewa garin na samun ruwa ne daga fanfo mai amfani da hasken rana guda daya.

Jibrin ya ce duk da cewa garin na da fanfunan tuka-tuka guda tara, sai dai gaba dayansu sun daina aiki kusan shekara daya baya, koma fiye da hakan.

Malam Babaji Jibrin

Malam Babaji Jibrin
Source: Original

"A yanzu muna da fanfo mai amfani da hasken rana guda daya ne kawai, wanda kowa a garin ke dibar ruwa daga gareshi. Sauran fanfunan tuka-tuka guda tara sun daina aiki kusan shekaradaya baya.

"Haka mafi yawanmu ke layi domin dibar ruwa, kusan karfe daya na dare, wasu kuma na dibar ruwan da misalinkarfe hudu na asuba, yayin da za ka taras da daruruwan mutane suna layin dibar ruwan da rana.

"Na ga yadda wasu gidaje ke kwana biyu ba tare da sun dora girkin abinci ba saboda karancin ruwa.

"Muna kira ga gwamnati da masu ruwa da tsaki da su taimaka su cece mu daga daga wannan matsalar ruwan da muke fama da ita," a cewar shugaban gargajiyar.

Mazi Huzaifa Yari

Mazi Huzaifa Yari
Source: Original

Ko da wakilan Legit.ng TV Hausa suka ji ta bakin wani mazaunin garin, Mr. Mazi Huzaifa Yari, ya ce da yawan mata da maza, da suka hada da kananan yara a garin, na ajiye ayyukansu na yau da kullum domin neman ruwa, wanda ya zama kamar Zinare wajen nema.

"Karancin ruwa a garinmu ya faru ne sakamakon rashin kawo ruwan fanfo akan lokaci, da kuma karancin rijiyoyi a garin, duk da cewa, mafi yawan rijiyoyin basu wani tara ruwa balle har ya ishi mutane da yawa.

"Fanfon da muke da shi ba zai iya wadatar da adadin mutanen da ke rayuwa a garin, sama da mutane 1,000 ke rayuwa a garin, kan fanfo hudu, a tankin ruwa daya, ba zai taba wadatar da wadannan mutane ba," a cewar Yari.

Da aka tuntube shi kan lamarin, Mr Ibrahim Bello, wani jami'i a hukumar samar da ruwa tare da tsaftace shi a kauyuka da karkara (RUWASSA), ya ce sam hukumar ba ta da masaniya kan wannan matsala da al'ummar Tudun Wus ke fama da ita ta karancin ruwa.

Tudun Wus: Sama da mutane 1,000 ke fuskantar matsin rayuwa saboda karancin ruwa

Tudun Wus: Sama da mutane 1,000 ke fuskantar matsin rayuwa saboda karancin ruwa
Source: Original

Bello, wanda shi ne mataimakin babban manaja a sashen sadarwa da tsare tsare a RUWASSA, ya jaddada cewa hukumar ba ta karbi wani korafi daga al'ummar ba har yanzu.

"Ace wai su ce suna da fanfunan tuka-tuka har guda tara, kuma gaba daya basa aiki, ni a nawa ganin, akwai wani boyayyan lamari a maganar nan.

"Saboda idan har da gaske suke, da tuni sun kawo korafinsu. Wannan bakon labari ne a wajena, amma zamu gudanar da bincike nan ba da jimawa ba, kuma zamu dauki mataki akai," a cewar Bello.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Tudun Wus: Rayuwa a garin da babu ruwa | Legit TV Hausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel