Rundunar 'yan sanda ta kama kasurgumin dan fashin da ya taba kwace bindigar DSP

Rundunar 'yan sanda ta kama kasurgumin dan fashin da ya taba kwace bindigar DSP

A yayin hutun karshen makon nan ne rundunar 'yan sanda a jihar Anambra ta bayyana cewar ta samu nasarar kama wani kasurgumin dan fashi da makami, Chinedu Ani, wanda ya taba yiwa wani babban dan sanda mai mukamin DSP fashi a kauyen Idodo dake kan hanyar Enugu zuwa Abakaliki tare da kwace masa bindiga.

A cikin wani jawabi da ya fitar, kakakin rundunar 'yan sadan jihar Anambra, DSP Haruna Mohammed, ya ce 'yan sandan rundunar SARS sun samu nasarar kama Ani da misalin karfe 11:00 na safiyar ranar Asabar a wata mobooya dake Obosi a karamar hukumar Idemili ta Kudu dake jihar Anambra.

Kakakin ya kara da cewa Ani, mai shekaru 28 a duniya, dan asalin karamar hukumar Nkana ta Gabas ce dake jihar Enugu.

Rundunar 'yan sanda ta kama kasurgumin dan fashin da ya taba kwace bindigar DSP

Wasu gungun masu garkuwa da mutane da rundunar 'yan sanda tayi bajakolin su ranar Alhamis
Source: Facebook

"Mai laifin tare da wasu abokan sa da har yanzu rundunar 'yan sanda ke nema sun taba yiwa jami'in dan sanda DSP Tochukwu Ogalagu fashi da misalin karfe 8:15 na daren ranar 10 ga watan Maris, 2019, a kauyen Idodo dake kan hanyar Enugu zuwa Abakaliki tare da kwace masa karamar bindigar sa mai lamba kamar haka AO8185Z," a cewar kakakin.

LABARAI MASU ALAKA: Rundunar 'yan sanda ta kama wadanda suka yi garkuwa da surukar Masari

An kama 'yan Boko Haram 4 da suka gudu zuwa jihar Edo

Rundunar 'yan sanda tayi bajakolin masu garkuwa da mutane 93 da suka fitini hanyar Abuja

A cewar DSP Mohammed, bayan ya sha matsa a ofishin 'yan sanda, mai laifin ya jagoranci rundunar 'yan sanda zuwa kauyen Ezeama dake karamar hukumar Nkana ta Arewa a jihar Enugu inda ya boye bindigar DSP Ogalagu.

"Har yanzu mu na cigaba da gudanar da bincike a kan lamarin tare da cigaba da kokarin ganin ragowar abokan sa da suka gudu sun shiga hannu domin su fuskanci hukunci," in ji DSP Mohammed.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel