Mona Mustapha Audu zai bar YPP ya tsaya takarar Gwamna a APC

Mona Mustapha Audu zai bar YPP ya tsaya takarar Gwamna a APC

Mun ji cewa yaron Marigayi tsohon gwamnan jihar Kogi Prince Abubakar Audu watau Mona Mustapha Audu, ya daura damarar tsayawa takara a zaben jihar da za ayi a karshen wannan shekara ta 2019.

Mona Mustapha Audu ya fara shirin sauya-sheka daga jam’iyyar hamayya ta YPP, ya koma APC domin neman tikitin takarar gwamna a zaben na bana. Hakan na nufin Audu zai nemi karbe tikitin jam’iyyar APC a hannun Gwamna ma-ci.

Daily Trust ta rahoto cewa Yaron Marigayin yana daf da komawa APC mai mulki domin cin ma burinsa da kuma na Mahaifinsa. An fara wannan rade-radin ne bayan an ga Mustapha Audu ya gana da wasu manya a cikin gwamnatin APC.

Rahotanni sun nuna cewa Mustapha Audu ya gana da Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha da kuma wani Mai ba shugaban kasa shawara a kan harkokin siyasa watau Hon. Gidado Samani kwanan nan a babban birnin tarayya Abuja.

KU KARANTA: Ministoci sun fara lalube cikin duhu a game da nadin da Buhari zai yi

Wannan surkule da Yaran tsohon gwamnan yake yi bai rasa nasaba da yunkurin karawa da gwamna Yahaya Bello mai neman tazarce a jam’iyyar APC. APC na iya ba Mona Audu tikiti a zaben na bana a dalilin rasuwar Mahaifinsa.

Idan ba ku manta ba tsohon gwamna Prince Abubakar Audu, ya rasu ne ana daf da sanar da sakamakon zabe. Wannan ya sa INEC ta bayyana Yahaya Bello a matsayin wanda zai gaji nasarar tsohon gwamnan, wanda wasu ba su ji dadi ba.

Akwai dai yiwuwar jam’iyyar APC ta bada tutar ta wannan karo ga yaron na Marigayi Audu domin ya jarraba sa’ar sa a babban zaben da za ayi a Watan Nuwamban bana da nufin fanshewa Mahaifinsa.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel