Kwanan nan za a rika karbar VAT a kasuwancin yanar gizo - Fowler

Kwanan nan za a rika karbar VAT a kasuwancin yanar gizo - Fowler

Mun ji cewa Hukumar FIRS ta Najeriya mai karbar haraji ta bayyana cewa nan ba da dadewa ba, za a rika biyan haraji na VAT daga duk wani cinikayya da aka yi ta shafukan cefane da ke yanar gizo.

Shugaban hukumar FIRS, Mista Babatunde Fowler, ya bayyana wannan a lokacin da ya zanta da wasu manema labarai Ranar Asabar dinnan 18 ga Watan Mayu a Birnin New York da ke kasar Amurka.

Mista Babatunde Fowler yake cewa ya kamata ace bankuna su na tatsar wannan haraji a duk wani ciniki da aka yi ta yanar gizo. A cewar Babatunde Fowler wannan irin haraji ba wani sabon abu bane.

Fowler yake cewa hukmar FIRS za tayi kokari wajen ganin ana karbar duk wani haraji na VAT a wajen hada-hadar kaya da sauran su ta kafafen yanar gizo. Wannan shiri zai taimakawa asusun Najeriya.

KU KARANTA: Karin albashin Ma'aikata ya jefa Gwamnatin Najeriya a matsi

Kwanan nan za a rika karbar VAT a kasuwancin yanar gizo - Fowler

Shugaban FIRS Tunde Fowler yace za a sa VAT a cikin cinikin yanar gizo
Source: Depositphotos

Hukumar FIRS ta ci burin samun Naira Tiriliyan 8 na haraji daga hannun jama’a a shekerar nan ta 2019, wannan ya sa ake faman kokarin kawo hanyoyi da dabaru da za a rika samun kudin shiga a Najeriya.

Daga cikin dabarun da FIRS ta kawo domin cin ma wannan buri akwai rangwame da aka bada na yi wa kamfanoni rajista, wanda bayan nan za ayi ram da duk wanda ya saba doka, kuma a yake masa tara.

Mista Fowler yake cewa FIRS za ta samu Biliyan 750 zuwa Naira Tiriliyan 1 daga matakin da za su dauka na hukunta wadanda su ke saba doka na gujewa biyan harajin da ke kan su a Najeriya.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel