Rashin tsaro: Gwamna Bagudu ya nemi hadin kan al'umma a jihar Kebbi

Rashin tsaro: Gwamna Bagudu ya nemi hadin kan al'umma a jihar Kebbi

Gwamnan jihar Kebbi Abubakar Atiku Bagudu, a ranar Asabar da ta gabata, ya yi kira na neman hadin gwiwar al'ummar kasa a kan tallafawa gwamnatin tarayyar Najeriya wajen magance kalubalai na rashin tsaro.

Kamar yadda majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito, gwamna Bagudu ya kuma nemi al'ummomin kasar nan a kan bayar da tallafin rahotanni da kuma bayanai musamman ga hukumomin tsaro da za su agaza masu wajen dakile aukuwar ta'addanci da kuma sauke nauyin da rataya a wuyan su.

Gwamnan jihar Kebbi; Abubakar Atiku Bagudu

Gwamnan jihar Kebbi; Abubakar Atiku Bagudu
Source: Depositphotos

Yayin babatu dangane da yadda lamari na rashin tsaro ya ci tura tare da kaiwa intaha a kasar nan, gwamna Bagudu ya ce magance wannan mummunar annoba da ta zamto ruwan dare a kasar nan musamman a Arewacin Najeriya yaki ne na mu duka da bai takaita kadai a kan gwamnati ba.

Kasancewar sa babban bako na musamman, furucin gwamna Bagudu na zuwa ne yayin halartar laccar Azumi a ranar 12 ga watan Ramadana wadda Ministan bayanai da al'adu, Alhaji Lai Muhammad ya dauki nauyin shiryawa a karamar hukumar Irepodun ta jihar Kwara.

KARANTA KUMA: Ta'addancin Boko Haram da Makiyaya manufa ce ta musuluntar da Najeriya - Obasanjo

Gwamna Bagudu ya yi tsokaci da cewar rashin tsaro a kasar nan ba gazawa ba ce ta gwamnati illa iyaka a tashi a farga wajen mara mata baya yayin da ta ke iyaka bakin kokarin ta domin ganin tattalin arzikin kasa ya bunkasa.

A karshe gwamnan jihar Kebbi ya yi kira ga dukkanin al'ummar Najeriya ba tare da bambamcin addini ba a kan su daura damara tare da sanya sulken bai wa gwamnatin tarayya mafificin hadin kai domin tsarkake kasar nan daga dukkanin wani kalubale na rashin tsaro.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta a Facebook ko kuma Twitter:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi: https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel