Ta'addancin Boko Haram da Makiyaya manufa ce ta musuluntar da Najeriya - Obasanjo

Ta'addancin Boko Haram da Makiyaya manufa ce ta musuluntar da Najeriya - Obasanjo

Yayin babatu da bayyana rashin jin dadin ci gaba da ta'azzarar ta'addancin kungiyar masu tayar da kayar baya ta Boko Haram da kuma fitintinu na makiyaya, tsohon shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo ya bayyana babbar manufar su a Najeriya.

A cewar tsohon shugaban kasa, wannan kalubalai da Najeriya ke fuskanta halin yanzu sun sha gaban duk wani karfi na gwamnati a sakamakon hadin gwiwar mayakan Boko Haram da kungiyar ta'adda mafi muni a ban kasa dake cin karen ta babu babbaka a yankin Afirka ta Yamma.

Tsohon shugaban kasar Najeriya; Cif Olusegun Obasanjo

Tsohon shugaban kasar Najeriya; Cif Olusegun Obasanjo
Source: UGC

Cikin kalaman sa, tsohon shugaban kasa ya ce a halin yanzu babu wani batu na rashin ilimi, rashin aiki ko kuma katutu na talauci a tsakanin matasa da yake ci gaba da rura wutar ta'addanci a Najeriya face miyagun ababe dake aukuwa da manufa ta musuluntar da nahiyyar Afirka baki daya.

Jaridar The Punch ta ruwaito hakan cikin jawaban da tsohon shugaban kasa Olusegu ya gabatar, yayin halartar babban taron hudubar mabiya mazhabar Anglican na addinin Kirista a karamar hukumar Isoko ta Kudu da ke jihar Delta a ranar Asabar.

Tsohon shugaban kasar ya yi kira na neman tashi tsaye wurjajan wajen fuskantar kalubalai na rashin tsaro inda a cewar sa gwamnatin ba ta biyo hanyar da ta dace ba wajen magance ta'addancin Boko Haram da kuma na Makiyaya tun fil azal.

KARANTA KUMA: Majalisar Dattawa ta amince da sauya ranar Dimokuradiya a Najeriya

Da ya ke ci gaba da kalubalantar gwamnatin Najeriya ta fuskar gazawar ta wajen inganta jin dadin dakarun soji da kuma gazawar ta wajen samar da ingatattun makamai da horaswa managarciya, Obasanjo ya ce ta'addancin kungiyar Boko Haram tuni ya sha gaban kasar nan a sakamakon hadin gwiwar ta da mafi munin kungiyar ta'adda a doron kasa ta ISIS, Islamic States of Iraq and Syria.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta a Facebook ko kuma Twitter:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi: https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel