Wata sabuwa: Gawar jaririya tayi sama ko kasa a wani asibiti dake Ondo

Wata sabuwa: Gawar jaririya tayi sama ko kasa a wani asibiti dake Ondo

-Gawar wata diya sabuwar haihuwa tace dauke ni inda ka ajiye ni a asibitin kwararru na jihar Ondo.

-Jami'in hulda da jama'a na hukumar yan sandan jihar Ondo ya tabbatar mana da aukuwar wannan lamari inda yace sun fara gudanar da bincike akan wannan lamarin.

Gawar jinjira sabuwar haihuwa tayi sama ko kasa a dakin ajiyar gawarwaki na asibitin kwararru dake jihar Ondo.

Jinjirar da mahaifiyarta dai sun mutu ne ranar Laraba a asibitin ‘yan sanda dake Akure yayinda da uwar ke nakuda.

Wata sabuwa: Gawar jaririya tayi sama ko kasa a wani asibiti dake Ondo

Wata sabuwa: Gawar jaririya tayi sama ko kasa a wani asibiti dake Ondo
Source: Facebook

KU KARANTA:Zamana a gidan yari –Zainab Aliyu

Bayan mutuwarsu ba tare da daukar tsawon lokaci ba aka kai gawarwakin nasu dakin ajiyar gawa dake asibitin kwararru ta Ondo.

Wata majiya ta shaida mana a ranar Asabar da iyalan wannan mata suka isa asibitin domin daukar gawarwakin saboda su je zuwa yi masu jana’iza, sai suka tarar da gawar uwar kadai babu ta diyar wacce tayi sama ko kasa.

Majiyar ta kara da cewa, iyalan sun nuna rashin amincewarsu da wannan lamari inda suka nemi lallai a fito masu da gawar jinjirar tasu.

A bangaren hukumar yan sandan jihar kuwa tuni ta fara gudanar da bincike domin gano bakin zaren wannan matsalar da ta auku na batar gawar jaririyar.

Jami’in hulda da jama’a na hukumar ‘yan sandan jihar, Femi Joseph ya tabbar mana da aukuwar wannan lamari. Yace “ Zamu gayyaci ma’aikatan asibitin domin su amsa tambayoyinmu, har yanzu bamu kama mutum ko guda ba.”

A bangaren gwamnatin jihar kuwa, kwamishinan lafiya na jihar Ondo Wahab Adegbenro yace wannan badakkala na hannun yan sanda domin su gudanar da binciken da ya dace.

“ Mun riga da mun mika ma su kula da dakin ajiyar gawar zuwa ga hukumar ‘yan sanda domin a bincike su. Zamu zuba ido muga yadda binciken zai kaya.” Inji kwamishinan.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

KU LATSA : Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadan

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel