Da sauran rina a kaba: Karin albashi ya sa Gwamnatin Najeriya a sarkakiya

Da sauran rina a kaba: Karin albashi ya sa Gwamnatin Najeriya a sarkakiya

Mun samu labari daga Jaridar Business Day mai kawo rahoto a kan labaran tattali da kasuwanci cewa har yanzu akwai sauran aiki kafin gwamnatin Najeriya ta shawo kan biyan sabon tsarin albashi.

A shekarar nan ne dai aka karkare batun karawa Ma’aikatan Najeriya mafi karancin albashi, wanda kuma tuni har shugaban kasa ya rattaba hannu a kan dokar da tace kowane ma’aikaci zai rika samun akalla N30, 000 duk wata.

Sai dai bincike ya nuna cewa biyan wannan sabon albashi, ba zai zo wa gwamnati da sauki ba, domin tsarin tattalin arzikin Najeriya na cikin-gida yana da rauni. Jaridar ta Business Day ta bayyana wannan a Ranar Juma’ar da ta wuce.

Rashin isasshen kudin-shiga zai sa Najeriya ta duba yiwuwar kara haraji na VAT domin a iya biyan kowane Ma’aikaci abin da bai gaza N30, 000 ba. Watakila kuma gwamnati ta tokare farashin Dalar Amurka a kan N305 a kasuwa.

KU KARANTA: Wasu Ma'aikatan Jihar Zamfara sun yi shekara 5 babu albashi

Da sauran rina a kaba: Karin albashi ya sa Gwamnatin Najeriya a sarkakiya

Raunin tattalin arzikin Najeriya ya bayyana bayan an amince da karin albashi
Source: Depositphotos

Wata hanya kuma da gwamnati ta ke dubawa wurin samun kudin da za a rika biyan albashi shi ne ta tallafin man fetur. Gwamnatin tarayya na iya daina biyan tallafin fetur wanda ke ci wa kasar biliyoyi, domin ta iya biyan albashin.

Rahoton na Ranar 17 ga Watan Mayu ya bayyana cewa albashin jami’an tsaro ya karu da sama da Naira Biliyan 250 a dalilin wannan kari da aka yi. Haka zalika Matasan da ke yi wa kasa hidima za su amfana da wannan karin albashi.

Kusan Naira Biliyan 70 gwamnati za ta kara a cikin kudin da ta ke kashewa a kan albashi idan aka soma biyan masu bautar kasa watau NYSC wannan sabon albashi N30, 000 a maimakon abin da su ka saba karba na N18, 000 duk wata.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel