Maniyyata za su kashe N1, 549,297.09 wajen sauke farali a Kaduna

Maniyyata za su kashe N1, 549,297.09 wajen sauke farali a Kaduna

Mun ji labari cewa Hukumar kula da walwala da jin dadin Mahajjata a jihar Kaduna, SMPWB, ta sanar da adadin kudin da za a biya domin zuwa kasa mai tsarki a sauke farali a wannan shekara ta 1440.

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta rahoto jiya Asabar, 19 ga Watan Mayun 2019, kudin aikin hajji ya karu a kan abin da aka biya a shekarar 2018 da ta gabata. Wannan shekara, Maniyyata za su kashe fiye da Naira Miliyan 1 da rabi.

Malam Yunusa Abdullahi, wanda shi ne jami’in da ke kula da harkokin yada labarai a SMPWB, ya bayyana cewa hukumar kula da hajji na kasa NAHCON, ta amince da N1, 549,297.09 a matsayin kudin kujera a Kaduna a bana.

Jami’in yada labaran hukumar Mahajjatan na Kaduna ya bayyana cewa an cin ma wannan matsaya ne bayan an lissafa kudin otel da za a zauna a Birane Makka da Madinah a kasae ta Saudi Araba. Ana kuma ba Mahajja kudin guzuri.

KU KATANTA: Akwai bukatar a sake duba batun kujerar Hajji a Najeriya

Shugaban da ke kula da wannan hukuma a jihar Kaduna, Imam Hussaini Ikara, ya tabbatar da cewa kowane Maniyyanci da ya tashi zai karbi Dala 800 a matsayin kudin da zai sa a aljihu domin yayi sayayya da guzuri idan a Saudi

Haka zalika wadanda su ka je aikin Hajji a cikin shekaru 4 da su ka wuce, za su biya wasu karin kudin har Riyal 2, 000 watau kusan N162, 000. Wannan karo kuma babu maganar karama da babbar kujera kamar yadda aka saba yi a baya.

Yanzu dai hukumar tana jawo hankalin masu niyya da su karasa biyan kudinsu kafin lokaci ya kure. Haka kuma ana bukatar Maniyyatan da su nemi takardun biza na shiga kasa mai tsarkin tun yanzu.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel