Babu shakka ana shiryawa Gwamnatin Buhari mugun nufi - Lai Mohammed

Babu shakka ana shiryawa Gwamnatin Buhari mugun nufi - Lai Mohammed

Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa tana da manyan shaidu da ke tabbatar da zargin da tayi kwanakin baya na cewa ‘yan adawa na bin gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari da sharri.

Kamar yadda mu ka samu labari a jiya Asabar 18 ga Watan Mayu, gwamnatin tarayya tace kukan da ta ke yi na cewa wasu ‘yan adawa sun shirya duk yadda za su hana shugaba Buhari mulkin kasar nan ba maganar wasa bace.

Ministan yada labarai da kuma al’adu na kasar, Lai Mohammed, ya bayyana wannan a wajen wani taron azumi da aka shirya a Garin Oro da ke jihar Kwara. Lai yace tabbas Atiku Abubakar da wasu ‘yan adawa su na ta faman tanadi.

Alhaji Lai Mohammed yake cewa sun gano hakan ne bayan wasu hujjoji da su ka bayyana a gare su na yadda manyan ‘yan adawar su ka shirya kawo hargitsi a kasar ta hanyar rugurguza tattalin arziki da kuma tada zaune-tsaye.

KU KARANTA: Kungiya ta taso INEC a gaba ta tabbatar da nasarar APC a zaben 2019

Babu shakka ana shiryawa Gwamnatin Buhari mugun nufi - Lai Mohammed

Ministan yada labarai da al’adu na Najeriya Lai Mohammed
Source: Depositphotos

Ministan yake cewa babu yadda za ayi gwamnati tayi tsit ganin irin hujjoji da bayanan da ta ke samu a kan irin kullin da Atiku da sauran Abokan hammaya su ke shiryawa bayan jam’iyyar PDP ta fadi zaben shugaban kasa da aka yi.

Daga cikin wadanda su ka halarci wannan taro da aka yi wa’azi aka kuma gabatar da lacca, akwai gwamnan jihar Kebbi, Atiku Bagudu da kuma Ministan sadarwa watau Adebayor Shittu kamar yadda Manama labarai su ka rahoto.

Ministan yayi tir da wannan shiri na ‘yan adawa inda yace faduwa zabe ta sa sun gaza hakuri su ajiye adawa a gefe, su rungumi kaddara, sai su ka buge da son rai a maimakon ganin cigaban Najeriya.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel