Mataki na gaba: Sauye-sauyen da Buhari zai yi a kunshin sabbin ministocin da zai nada

Mataki na gaba: Sauye-sauyen da Buhari zai yi a kunshin sabbin ministocin da zai nada

A yayin da ya rage saura kwanaki 10 a sake rantsar da shugaban kasa Muhammadu Buhari a matsayin zababben shugaban kasar Najeriya a karo na biyu, ministocin sa sun kara kaimi wajen matsin lamba da kamun kafa a wurin makusanta shugaba Buhari domin a sake koma wa gwamnati da su.

Rahotanni sun bayyana cewar a kalla kaso 70% na ministocin Buhari sun bar aiyukan su domin cigaba da shige-da-ficen ganin sun samu koma wa kujerun su. Sai dai wata majiya a fadar shugaban kasa ta bayyana cewar ministocin sun shiga kamun kafa ne saboda sun san cewar wannan karon shugaba Buhari ba zai dauki dogon lokaci ba wajen nada ministocin da zasu taya shi aiki.

Majiyar ta bayyana cewar shugaba Buhari zai jingine batun nan na tsuke yawan mukaman ministoci kamar yadda ya yi a zangon shi na farko.

"Bayan ministoci 36 da shugaban kasar zai nada; mutum guda daga kowacce jiha, ana saka ran cewar zai kara wasu ministocin guda 6; mutum daya daga kowanne yanki 6 na kasar nan.

"Bisa ga dukkan alamu, shugaban kasa ba zai bata lokaci ba wajen nada sabbin mukamai ba. A shirye yake ya aika sunayen sabbin ministocin da zai nada zuwa majalisa a watan Yuni don ya zuwa yanzu ya riga ya san mutanen da zai yi aiki da su a zangon sa na biyu," a cewar majiyar.

Mataki na gaba: Sauye-sauyen da Buhari zai yi a kunshin sabbin ministocin da zai nada

Buhari
Source: Facebook

Sannan majiyar ta kara da cewa babu wanda ya san sunayen su waye shugaba Buhari zai aike majalisa, hakan ne kuma ya tayar da hankalin ministocin sa na yanzu suka shiga kamun kafar na kusa da shi da kuma shugabancin jam'iyya.

A cewar majiyar, wannan karon shugaba Buhari zai raba ma'ikatar aiyuka, lantarki da gidaje zuwa ma'aikatu uku; ma'aikatar aiyuka, ma'aikatar lantarki da ma'aikatar gidaje, domin a samu damar gudanar da aiki a kowacce ma'aikata cikin sauki.

Kazalika ana saka ran cewar shugaban kasar zai fitar da ma'aikatar harkokin jiragen sama (Aviation) daga cikin ma'ikatar sufuri tare da mayar da ita ma'aikata mai cin gashin kan ta.

DUBA WANNAN: Saboda na soki Buhari aka kama ni - Malamin Islama

"Mai yiwuwa ma ya kirkiri ma'aikatar harkokin man fetur, sannan ya rushe mukamin karamin ministan harkokin man fetur," in ji majiyar.

Wata majiyar da ta nemi a sakaye sunan ta, ta bayyana cewar ta na da tabbacin cewa hatta wasu masu rike da mukamin siyasa da ake ganin na da kusanci da shugaba Buhari, basu da masaniyar ko zai sake koma wa da su a mulkin da zai yi a karo na biyu ko kuma canja su zai yi.

A cikin satin da zamu shiga ne ake saka ran shugaba Buhari zai yi taron majalisar zartar wa (FEC) na karshe da ministocin sa da hadiman sa.

Za a gudanar da taron FEC na musamman a ranar Litinin domin ministoci su samu damar gabatar da ragowar dukkan wata mukala da ta rage musu, sannan a gudanar da taro na karshe a wannan zangon na farko a ranar Laraba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel