Saboda na soki Buhari aka kama ni - Malamin Islama

Saboda na soki Buhari aka kama ni - Malamin Islama

A ranar Asabar ne Malamin Islaman nan, Mallam Idris Abdulaziz, dake garin Bauchi ya bayyana cewar jami'an tsaro na farin kaya (DSS) sun tsare shi ne bisa zargin sa da sukar shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Malamin addinin da aka sako shi ranar Juma'a ya shaida wa manema labarai cewar jami'an tsaron hukumar DSS sun shaida masa cewar yana sukar shugaba Buhari a cikin hudubar sa da sauran karatuttukan sa.

"Kuru-kuru suka fada min cewar ina zagin shugaban kasa a hudubobi na da majalisai kuma suna da hujja. Amma da na kalubalence su a kan su saka sautin murya ta domin jin wurin da na aikata hakan, sai suka kasa gabatar da hujja ko daya," a cewar sa.

Ya kara da cewa, ya shaida wa hukumar DSS cewar yana sukar gwamnati a kowanne mataki matukar tayi ba daidai ba, sannan ya kara da cewa ba zai ki shukar shugaba Buhari ba matukar ya yi kuskure.

Saboda na soki Buhari aka kama ni - Malamin Islama

Jami'an DSS
Source: UGC

"Na fada musu cewar na fi sukar tsohon shugaban kasa Goodluck Jonatahan idan aka kwatanta da sukar da nake yiwa shugaba Buhari. Na fada musu cewar ba zai yiwu na soki Jonathan a kan yin ba daidai ba amma na ki sukar Buhari ba saboda shi dan arewa ne kuma Musulmi bayan kuma jama'a na cikin wahala, idan nayi hakan ban yi adalci ba kuma ya saba da koyarwar addinini Islama," in ji Malam Idris.

DUBA WANNAN: Dankari: Majalisar dokokin jihar Bauchi tayi dokar hana kwace kudin sata

Malamin addinin ya kara da cewa daga bisani wani jami'in DSS ya zo ya kara yi masa tambayoyi a kan kungiyar bijilanti da ya kafa da kuma kasuwancin sa da ya gada a gidan su.

Malam Idris ya kara da cewa bayan ya sanar da su komai a kan kungiyar sa ta bijilanti da tsare-tsaren ta sai aka mayar da shi hedikwatar DSS dake Abuja, inda bayan sun sallame shi suka shaida masa yake ziyar hediwatar su dake Bauchi duk sati.

Kazalika, ya bayyana cewar bai hadu da Abu Amar ba, wani malamin addini daga jihar Katsina da hukumar ta DSS ke tsare da shi a Abuja.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel