Ganduje ya gabatar da shaidu 203 a kotu sauraron karrarakin zabe

Ganduje ya gabatar da shaidu 203 a kotu sauraron karrarakin zabe

Gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Ganduje ya gabatarwa kotu takardun kare nasararsa bayan karar da takarar gwamna na jam'iyyar PDP, Abba Kabir Yusuf na shigar na kallubalantar nasararsa a zaben ranar 23 ga watan Maris.

Gwamnan ya gabatarwa kotu takardun kare kansu dauke da shafukaka 1,800 da kuma shaidu 203 da za su taimaka wurin gamsar da kotu nasararsa.

A yayin da ya ke zantawa da manema labarai bayan gabatarwa kotun sauraron karrakin zabe hujjojin kare gwamnan, Musa Lawan, daya daga cikin lauyoyin gwamnan, ya ce babu gaskiya cikin karar da PDP ta shigar.

Ganduje ya gabatar da shaidu 203 a kotu sauraron karrarakin zabe

Ganduje ya gabatar da shaidu 203 a kotu sauraron karrarakin zabe
Source: Depositphotos

Kotun na zamanta ne a Miller Road, da ke unguwa Bompai a birnin Kano.

DUBA WANNAN: Yadda masu ciwon Ulcer za suyi azumin watan Ramadan cikin sauki - Masana

"Mun gabatarwa kotu takardun kare kanmu kuma mun kawo su a cikin lokacin da aka kayyade mana kuma muna fatan za muyi nasara. Tun farko, mun ce shigar da kara kotun ba shi da amfani."

Lauyan ya ce za su gabatarwa kotun muhimman shaidu 203 da za su bayar da shaida a kotun da zai nuna tabbas anyi zabe a Kano kuma hakan zai sa ayi watsi da zargin na jam'iyyar PDP.

Ya kara da cewa sun gabatar da takardun kare kansu a cikin wa'addin lokacin da aka diba musu kuma ya yi ikirarin cewa ko jam'iyyar PDP ta dauki lokaci kafin shigar da karar ta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku Latsa: Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadana

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel