Obasanjo ya sake yiwa Buhari kaca-kaca kan batun tsaro

Obasanjo ya sake yiwa Buhari kaca-kaca kan batun tsaro

- Tsohon shugaban kasa Obasanjo ya zargi Shugaba Buhari da yin sakaci a kan batun tsaro a Najeriya

- Obasanjo ya ce gwamnati mai ci yanzu ba ta dauki matakan da ya dace ba da yanzu halin rashon tsaron bai tabarbare ba

- Tsohon shugaban kasa na mulkin sojan ya ce kamata ya yi Buhari ya nemi taimako daga cikin gida da kasashen waje domin magance matsalar

Tsohon shugaban kasa Obasanjo ya sake cacakar shugaban kasa Muhammadu Buhari kan batun kallubalen rashin tsaro da ke fama da shi a sassan Najeriya.

Nigerian Tribune ta ruwaito cewa Obaanjo ya soki shugaban kasar ne yayin da ya ke jawabi a Cocin St. Paul da ke Oleh a karamar hukumar Isoko ta Kudu na jihar Delta.

A cewar rahoton, tsohon shugaban kasar zargi shugaban Buhari ya yin sakaci da batun Boko Haram da 'yan bidiga masu garkuwa da mutane da kai hare-hare.

Obasanjo ya sake yiwa Buhari kaca-kaca kan batun tsaro

Obasanjo ya sake yiwa Buhari kaca-kaca kan batun tsaro
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Na hannun daman Atiku ya bukaci a bayyana sunayen masu shirin juyin mulki

A kan rashin tsaro, dattijon ya ce, "Dole ne a dauki tsatsauran mataki a kan batun tsaro a kowanne makaki ba tare da nuna bangaranci ba."

Ya kara da cewa: "Ba a dauki mataki a kan lamarin Boko Haram da makasa ba tun da farko.

"Yanzu sun girma sun bunkasa sun kai matsayin da Najeriya kadai ba za ta iya magance abin ba. Yanzu sun hada kai da kungiyoyin ta'addanci na kasa da kasa na ISIS.

"Yanzu ba batun rashin ilimi bane ko rashin aikin da muke fama da shi da farko ba. Yanzu musuluntar da Africa ake kokarin yi tare da safarar mutane da kudade, safarar miyagun kwayoyi, safarar makamai, hakar ma'adinai ba bisa ka'ida ba da canjin gwamnati.

"Ya kamata a dauki mataki da wuri amma sai aka yi tsamanin Boko Haram matasa ne kawai masu neman tayar da hankula kuma ba a dauki matakan da suka da ce ba.

"A lokacin da muka gane matsalar da muke ciki, wasu tsiraru sun mayar da harkar damar shigo da tsaffin makamai da bindigogi da sojojin mu ba za su iya amfani da shi ba a yanzu."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku Latsa: Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadana

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel