Ameachi ya shawarci 'yan kabilar ibo a kan shugabancin kasa a 2023

Ameachi ya shawarci 'yan kabilar ibo a kan shugabancin kasa a 2023

Ministan Sufuri, Rotimi Ameachi ya ce wadanda ba su goyi bayan jam'iyyar All Progressive Congress (APC) ba su da ikon neman a basu shugabancin kasa a 2023.

Najeriya tana da manyan kabilu guda uku ne amma kabilar ibo ba su taba samun shugaban kasa ba tun dawowa mulkin demokradiyya a 1999.

A hirar da ya yi da jaridar The Sun, Ameachi ya ce ibo ba za su samu shugaban kasa ba saboda ba su da wani gudunmawar da za su kawo a 2023.

Ku manta da batun shugabancin kasa a 2023 - Ministan Buhari ya fadawa Ibo

Ku manta da batun shugabancin kasa a 2023 - Ministan Buhari ya fadawa Ibo
Source: Facebook

DUBA WANNAN: Rundunar soji ta fitar da jawabi a kan zargin yunkurin kifar da gwamnatin Buhari

Ya ce: "Ban san abinda za suyi ba tunda sun ki zaben jam'iyyar APC.

"Saboda juyawa APC baya da su kayi, ba su da ikon su zo su nemi kujerar shugabancin kasa.

"Idan da ibo sun fito sun zabi APC, za su iya zuwa su fadawa shugaban kasa da shugaban jam'iyya na kasa cewa a bawa Kudu maso gabas kujerar shugabancin kasa tunda a bawa sauran sassan a baya. Amma a yanzu wace hujja Kudu maso gaba suke da shi domin a basu shugabancin kasa a 2023?"

Ya ce hanya daya da za a iya samun dan takarar shugaban kasa daga kabilar Ibo shine idan an kafa wata kungiyar siyasa da za ta ratsa kauyuka wurin talakawa.

"Akwai bukatar su hada kansu wuri guda, su kafa mutane a matakin kananan hukumomi da jiha da za su rika haduwa lokaci zuwa lokaci.

"Ya kuma kamata su nemi kudi da za a tafiyar da jam'iyyar. Idan akayi hakan APC za ta cigaba da mulkin Najeriya amma ya zama dole kowa ya shigo a dama da shi. Ya kamata mu shigo cikin jam'iyya a dama da mu ba wai mu ware muna yin taro ba."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku Latsa: Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadana

Source: Legit

Mailfire view pixel