Hukumar DSS ta gargadi masu kokarin juyin mulki gabannin rantsar da Buhari

Hukumar DSS ta gargadi masu kokarin juyin mulki gabannin rantsar da Buhari

- Hukumar tsaro na farin kaya (DSS) ta yi gargadi ga wadanda ke kira ga sauyi a mulki

- Gargadin na zuwa ne yan kwanaki kadan bayan rundunar soji ta nesanta kanta daga wani shiri na juyin mulki

- Hukumar na hannun ka mai sanda ne ga wata kungiya karkashin inuwar Nigeria Continuity and Progress (NCP)

Rundunar tsaro na farin kaya (DSS) ta yi gargadi ga wadanda ke kira ga sauyi a mulki yayinda ake shirye-shiryen rantsar da Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar 29 ga watan Mayu.

Hukumar Hukumar na hannun ka mai sanda ne ga wata kungiya mai suna Nigeria Continuity and Progress (NCP).

Gargadin na zuwa ne yan kwanaki bayan rundunan Sojin Najeriya ta nesanta da kanta daga shirin juyin mulki.

Hukumar DSS ta gargadi masu kokarin juyin mulki gabannin rantsar da Buhari

Hukumar DSS ta gargadi masu kokarin juyin mulki gabannin rantsar da Buhari
Source: UGC

Hukumar DSS a wani jawabi da ta gabatar a ranar Juma’a tace: “A bayyane yake cewa wata gurbatacciyar kungiya da mambobin kungiyar na shirye shiryen yada tashin hankali akan gwamnati don aiwatar da aniyyar su na canja gwamnati da karfi da yaji.

“Bayan goyon bayan kafa ingantacciyar damukardiyya a Najeriya da kungiyar ta DSS ke yi, ba kuma zata yi wasa ba wajen magance mutane ko kungiya dake da aniyar haddasa rigingimun rashin zaman lafiya a hadin kai da zamantakewar kasar.

KU KARANTA KUMA: Ba zan iya goyon bayan kacaccala masarautar Kano ko kuma adawa da Ganduje ba – Shettima

“Haka zalika, Hukumar baza ta amince da ayyukan da suka saba ma doka ba ko tsare-tsaren da wassu tsagirun mutane ko kungiyoyi suka kafa don hargitsa hukumomin gwamnati.

“Cikin umurni, za a hukunta wadanda suka saba ma doka”.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel