Ba zan iya goyon bayan kacaccala masarautar Kano ko kuma adawa da Ganduje ba – Shettima

Ba zan iya goyon bayan kacaccala masarautar Kano ko kuma adawa da Ganduje ba – Shettima

- Kashim Shettima na jihar Borno ya bayyana cewa ba zai iya goyon bayn kowani bangare ba kan kafa sabbin masarautu a Kano ba

- Gwamna Ganduje ya amince da rarraba masarautun Kano

- Shettima ya bayyana cewa akwai alaka ta musamman a tsakaninsa da Ganduje da kuma Sanusi

Gwamna Kashim Shettima na jihar Borno, yace ba zai iya goyo bayan Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ko Sarki Muhammad Sanusi II ba, kan kafa sabbin masarautu a Kano.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa gwamnan, yayinda yake amsa tambayoyi daga manema labarai bayan taron kungiyar gwamnonin Arewa a Kaduna a ranar Juma’a, 17 ga watan Mayu yace ba zai taba Magana don goyon bayan kacaccala masarautar Kano ba ko kuma yayi adawa da gwamnan ba saboda yana da alaka ta musamman da Ganduje da kuma Sanusi.

Ba zan iya goyon bayan kacaccala masarautar Kano ko kuma adawa da Ganduje ba – Shettima

Ba zan iya goyon bayan kacaccala masarautar Kano ko kuma adawa da Ganduje ba – Shettima
Source: Twitter

Legit.ng ta tattaro cewa yace an sauya kanen maganganun da yayi a baya game da lamarin gaba daya.

Yace: “Zancen gaskiya shine, Gwamna Ganduje ya dauki nauyin karatun wasu marayu 200 dga jihar Borno wadanda Boko Haram suka kashe iyayensu tun daga matakin Firamare har zuwa jami’a. A daya bangaren, Sarkin Kano ne babban wanda ya hada mu da Alhaji Aliko Dangote.

KU KARANTA KUMA: Buhari ya manta da mu bayan cin zabe: Magoya baya

“A 2016, sarkin ya kasance a Borno sannan da ya ga halin da yan gudun hijira ke ciki, sai yayi Magana da Alhaji Aliko Dangote sannan Dangote ya kasance a jihar Borno sama da sau uku."

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel