Kakakin majalisa: Wata kungiyar kudanci na goyon bayan Gbajabiamila

Kakakin majalisa: Wata kungiyar kudanci na goyon bayan Gbajabiamila

-Wata kungiyar kudanci Najeriya ta goyi bayan Femi Gbajabiamila a matsayi wanda ya dace ya kasance sabon kakakin majalisar wakilai ta kasa

Wata kungiya ta yan kudu maso gabashin Najeriya mai suna South East Consultative Initiative (SECI) ta goyi bayan Femi Gbajabiamila a matsayin wanda zai kasance kakakin majalisar wakilai ta kasa.

Kungiyar tace, dan takarar da take goyon baya yana da duk abinda ake bukata na kasancewa kakakin majalisar wanda zai kawo ma kasar nan cigaban da take bukata.

Kakakin majalisa: Wata kungiyar kudanci na goyon bayan Gbajabiamila

Kakakin majalisa: Wata kungiyar kudanci na goyon bayan Gbajabiamila
Source: UGC

KU KARANTA:Yan sandan Binuwe sun kama mutum 30 cikin mako guda

Kungiyar ta fitar da wannan batun ne ta hannun shugabanta mai suna Nnaji Paschal ranar Asabar bayan ta kammala wata ganawa a Abakaliki babban birnin jihar Ebonyi. Kazalika kungiyar tayi watsi da danganta ta da ake na cewa tana goyon bayan Mista Emeka Nwajiuba a matsayin kakakin majalisar.

Amma ita wannan kungiya cewa tayi, “ Nwajiuba ba dan jam’iyar APC mai mulki bane, a don haka bai cancanci a bashi wannan kujera ba. Ba ma PDP yake ba yana a wata jam’iya ne mai suna Accord party”.

Kungiyar ta bayyana Gbajabiamila a matsayin mutum jajirtacce wanda bai da son kai cikin al’amuransa. Wannan dalilin ne yasa ya zama kan gaba a matsayin wanda yafi dacewa da ya ja akalar majalisar wakilai ta 9.

“ A shekarar 2015 yaso wannan kujera, amma daga bisani ya hakura ya kasance shugaban masu rinjaye na majalisar. A tunanin mu yayi hakan ne saboda maslahar majalisar da kuma ‘yan kasa baki daya. A don haka yanzu lokaci yayi da ya kamata takwarorinsa su saka masa bisa kyakkyawan aikin da yayi a baya.” A cewar wannan kungiyar.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

KU LATSA : Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadan

Source: Legit Nigeria

Tags:
Mailfire view pixel