Jonathan ya fadawa 'yan Najeriya gudunmawar da za su bayar don samar da tsaro

Jonathan ya fadawa 'yan Najeriya gudunmawar da za su bayar don samar da tsaro

- Tsohon shugaban kasa Dr Goodluck Jonathan ya bukaci 'yan Najeriya su yiwa gwamnati addu'o'i don shawo kan kallubalen tsaro da ke adabar kasar

- Tsohon shugaban kasar kuma jigo a jam'iyyar PDP ya ce lamarin tsaro ya dauki sabon salo a kasar

- Jonathan kuma ya musanta zargin da ake masa na cewar ya wawushe biloyoyin naira daga asusun kasa yayin da ya ke kan karagar mulki

Tsohon shugaban kasar Najeriya Dakta Goodluck Jonathan ya bukaci 'yan Najeriya su tallafawa gwamnatin tarayya da addu'o'i domin samun nasarar kawar da matsalar garkuwa da mutane, ta'addanci da hare-haren 'yan bindiga a sassan kasar.

Ya ce batun garkuwa da mutane ba ta'addanci ba sabon abu bane a kasar amma a yanzu lamarin ya dauki sabon salo kamar yadda kamfanin dillancin labarai NAN ta ruwaito.

Tsohon shugaban kasa Jonathan ya yi tsokaci kan kallubalen tsaro a Najeriya

Tsohon shugaban kasa Jonathan ya yi tsokaci kan kallubalen tsaro a Najeriya
Source: UGC

DUBA WANNAN: Na hannun daman Atiku ya bukaci a bayyana sunayen masu shirin juyin mulki

Legit.ng ta tattaro cewa Jonathan ya yi wannan jawabin ne a ranar Juma'a 17 ga watan Mayu a Abuja a cocin St Mathew da ke Gwarimpa a babban birnin tarayya, Abuja.

Tsohon shugaban kasar ya yi amfani da damar da ya samu domin nesanta kansa daga zargin cewa ya wawushe biliyoyin naira daga asusun kasa yayin da ya ke kan karagar mulki inda ya ce karya ake masa.

Ya kuma ce nasarorin da ya samu a tsawon mulkin kasar da ya yi na shekaru biyar sun faru ne saboda addu'o'i da taimakon Allah.

A baya, Legit.ng ta ruwaito cewa tsohon shugaban kasar ya shawarci 'yan Najeriya kada suyi kasa a gwiwa wurin addu'o'i domin cin galaba a kan kallubalen tsaro da ake fama da shi a kasar.

A sakonsa na Easter a ranar 18 ga watan Afrilu, Jonathan ya ce kasar tana da ikon kawo karshen bakin cik da halin rashin tsaro da ake fama da shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku Latsa: Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadana

Source: Legit

Mailfire view pixel