Fargaba: ‘Yan sanda sunyi nasarar tunbuke bamabamai biyu kan sun fashe a Anambra

Fargaba: ‘Yan sanda sunyi nasarar tunbuke bamabamai biyu kan sun fashe a Anambra

-Yan sanda sunyi nasarar cire bamabamai biyu a jihar Anambra ba tare da fashewarsu ba

-Wadannan bamabamai dai an same su ne a garin Amawbia wanda hakan ya jefa tsoro da halin firgici ga al'ummar yankin

Al’ummar Amawbia wacce ke kusa da Awka babban birnin jihar Anambra sun kasance cikin firgici a jiya Juma’a yayin da suka gano bamabamai biyu kafin su fashe.

Jami’in hulda da jama’a na hukumar yan sandan jihar SP Haruna Muhammad yace, “Mun samu labarin wadannan bamabamai ne ta bakin mazauna garin Amawbia wacce ke kusa da Awka babban birnin jihar Anambra.”

Fargaba: ‘Yan sanda sunyi nasarar tunbuke bamabamai biyu kan sun fashe a Anambra

Fargaba: ‘Yan sanda sunyi nasarar tunbuke bamabamai biyu kan sun fashe a Anambra
Source: UGC

KU KARANTA:Sha’anin tsaro: Sojin Najeriya sun tattauna da takwararsu ta kasar Nijar

A jawabin da jami’in ya rubuta kan batun cewa yayi “ A ranar 16 ga watan Mayun 2019 da misalin karfe 3:50 na yamma mu ka samu rahoto akan wasu bamabamai da basu riga sun fashe ba, wadanda aka samu a shiyyar Elu Orji dake kauyen Amawbia a karamar hukumar Awka ta kudu a jihar Anambra.

“Biyo bayan wannan rahoton ne, muka tura da jami’anmu wadanda suka kware akan tasge bam zuwa wannan wuri. Zuwan su wurin sun yi nasarar tasge wannan bamabamai ba tare an samu matsalar fashewarsu ba. Dadin dadawa sun tabbatar mana cewa bamabamai ne na yaki wadanda ba su riga sun fashe ba a lokacin.” A fadar kakakin.

A wani labari mai kama da wannan, wani kwamishinan jihar Ogun ya dawo kan kujerarsa bayan ya mika takardar murabus a ranar Talata.

Kwamishinan ya dawo aiki ne ranar Juma'a al'amarin da ya daurewa mutane da dama kai.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

KU LATSA : Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadan

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel