Buhari ya manta da mu bayan cin zabe: Magoya baya

Buhari ya manta da mu bayan cin zabe: Magoya baya

- Kungiyar 'yan gani kashe nin Buhari sun koka kan watsi da su da suka ce shugaban kasar ya yi bayan ya lashe zabe a 2015

- Shugaban kungiyar, Musa Inuwa ya ce sunyi gwagwarmayar ganin Buhari ya lashe zabe har da an kulle wasu daga cikinsu a kurkuku

- Inuwa ya kara da cewa 'yan Najeriya suna sa ran shugaban kasa ya dauki mataki musamman a fanin tsaro, lafiya da tattalin arziki

Kungiyar 'yan gani gashe nin Buhari sunyi korafi kan watsi da su da Shugaba Muhammadu Buhari yayi bayan ya yi nasarar lashe zaben shugaban kasa na 2015.

A hirar da ya yi da manema labarai a Kano, shugaban kungiyar, Musa Inuwa ya ce shugaban kasar bai saka musu hidimar da su kayi masa ba tun lokacin da ya fara takarar shugaban kasa a 2003 kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Buhari ya manta da mu bayan cin zabe: Magoya baya

Buhari ya manta da mu bayan cin zabe: Magoya baya
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Rundunar soji ta fitar da jawabi a kan zargin yunkurin kifar da gwamnatin Buhari

Legit.ng ta tattaro cewa Inuwa ya ce kungiyar tayi gwagwarmaya lokacin yakin neman zaben Buhari har da kai ga an kulle wasu daga cikinsu a gidan yarin Karshi saboda zanga-zangar goyon bayan shugaban kasa da su kayi a 2007.

Inuwa ya ce su ne suka yi shige da fice a lokacin da aka hana Buhari shiga Daura, "Mune, 'yan gani kashe nin Buhari muka yi gwagwarmayar ganin shi da tawagarsa sun shiga Daura ta kowane hali."

Ya yi ikirarin cewa Buhari ya zagaye kansa da mutanen da ba suyi gwagwarmaya tare da shi ba lokacin zabe kuma ba su kaunarsa.

Inuwa ya kara da cewa 'yan Najeriya suna sa ran shugaban kasa ya tabbuka abin azo a gani a fannin tsaro, lafiya da tattalin arziki.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku Latsa: Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadana

Source: Legit.ng

Online view pixel