PACEDA ta gargadi Gwamna Akeredolu kan neman hallasta amfani da ganyen wiwi

PACEDA ta gargadi Gwamna Akeredolu kan neman hallasta amfani da ganyen wiwi

Kwamitin bawa shugaban kasa shawara a kan kawar da amfani da miyagun kwayoyi, PACEDA ta ce duk wata yunkuri da ake yi na hallasta amfani da ganyen wiwi ta kowanne fani a Najeriya ba zai ci nasara ba saboda gwamnati da dukufa wurin magance kallubalen ta'amulli da miyagun kwayoyi.

Wannan gargadin yana zuwa ne a ranar Juma'a kwanaki hudu bayan gwamna Rotimi Akeredolu na jihar Ondo ta shawarci gwamnatin tarayya ta goyi bayan noma ganyen wiwi domin amfani da shi wurin yin magunguna a kasar.

Shugaban PACEDA kuma tsohon shugaban mulkin soji na jihar Legas, Janar Mohammed Marwa (mai murabus) ya ce kuskure ne kokarin da wasu keyi na neman hallasta amfani da ganyen wiwi.

FG ta gargadi gwamnan da ke neman hallasta noma da amfani da wiwi

FG ta gargadi gwamnan da ke neman hallasta noma da amfani da wiwi
Source: UGC

DUBA WANNAN: Na hannun daman Atiku ya bukaci a bayyana sunayen masu shirin juyin mulki

Punch ta ruwaito cewa Gwamna Akeredolu ya ce noman ganyen wiwi zai iya samar wa dubban matasan Najeriya aikin yi tare da inganta tattalin arzikin kasar a yayin da ya ke shawartar gwamnatin tarayya ta amince da batun.

Sai dai Marwa ya yi watsi da wannan rokon inda ya ce ba za a amince da samun kudi ba idan dai rayukkan 'yan Najeriya zai shiga hatsari sakamakon yawaitan ganyen wiwi a kasar.

Ya ce: "Abin tsoro ne wasu su nemi a hallasta noma da amfani da ganyen wiwi a Najeriya a wannan lokacin da kimanin 'yan Najeriya miliyan 10 suna tu'amulli da wiwi.

"Kwamitin mu ta kwashe watanni shida tana zuwa sassan kasar nan domin nazarin hadarin da ganyen wiwi ke yiwa mutane musamman matasa da kuma nemo hanyoyin magance matsalar.

"Babu shakka, Shugaba Muhammadu Buhari ya damu da batun shi yasa ya kafa PACEDA domin a nemo hanyar magance matsalar baki daya. Saboda haka ba zamu nade hannu mu bari wasu mutane su kawo cikas ga yunkurin da gwamnati keyi ba domin ciyar da kasa gaba."

Ya kara da cewa, "Ba zamu amince da duk wata hanyar habbaka tattalin arziki da ka iya jefa rayuwar 'yan Najeriya cikin fitina ba. Akwai bukatar dukkan masu ruwa da tsaki su hada hannu wurin magance matsalar a maimakon yin akasin hakan."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku Latsa: Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadana

Source: Legit

Mailfire view pixel