DSS ta saki shahararren malamin Musulunci na Katsina, sa’o’i 48 bayan kama shi

DSS ta saki shahararren malamin Musulunci na Katsina, sa’o’i 48 bayan kama shi

- Sa’o’i 48 bayan kama shi, hukumar DSS ta saki shahararren Malamin Musuluncin nan, Aminu “Abu Ammar” Usman

- Anyi zargin cewa an kama malamin ne bayan wani fatwa da yayi inda ya caccaki gwamnatin Buhari

- An rahoto cewa Usman ya tabbatar da sakin nasa, inda ya bayyana cewa jami’an DSS ne suka dawo dashi gida

Bayan shafe sa’o’i 48 a tsare a hannun rundunar tsaro na farin kaya (DSS), an saki shahararren malamin nan na Musulunci da ke da zama a Katsina, Aminu “Abu Ammar” Usman, a daren ranar Juma’a, 17 ga watan Mayu.

A cewar jaridar Daily Trust, hukumar DSS sun gayyacci malamain sannan suka tsare shi, bayan wani fatawa da ya bayar inda ya caccaki gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari kan tabarbarewar tsaro a fadin kasar.

DSS ta saki shahararren malamin Musulunci na Katsina, sa’o’i 48 bayan kama shi

DSS ta saki shahararren malamin Musulunci na Katsina, sa’o’i 48 bayan kama shi
Source: UGC

Legit.ng ta tattaro cewa Usman ya tabbatar da sakin nasa a wani hira ta wayar tarho. Ya kuma tabbatar da cewa an gayyace shi sannan an tsare shi saboda hudubar da yayi wanda ya shahara.

Yace: “Eh, an sake ni a jiya kusan lokacin bude baki. Jami’an DSS ne suka kawo ni gida.”

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Jami’an rundunar yan sandan farin kaya sun gayyaci wani malamin addinin Musulunci mazaunin Katsina, Mallam Aminu Usman wanda aka fi sani da Abu Ammar, sannan sun tsare shi.

KU KARANTA KUMA: Tsohon Shugaban kasa Ibrahim Babangida na nan da ransa bai mutu ba - Maiyoyi

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Abu Ammar na tare da abokinsa, Malam Shamsu, lokacin da ya amsa kiran gayyata daga jami’an tsaro wanda suka nemi ya zo ofishin DSS da ke jihar.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel