Tirkashi: Wani kwamishina yayi amai ya lashe a jihar Ogun

Tirkashi: Wani kwamishina yayi amai ya lashe a jihar Ogun

-Kwamishinan da yayi murabus daga aiki a Ogun ya dawo kan kujerarsa bayan kwana biyu da rubuta takardar barin aikin nasa

-A cewarsa, gwamna Ibikunle Amosun ne yaki amincewa da takardar kuma korafin da yayi an magancesa a yanzu

An samu cecekuce ranar Juma’a a jihar Ogun yayinda kwamishinan kananan hukumomin jihar Cif Jide Ojuko yace, Ibikunle Amosun yaki amincewa da takardar ajiye aikin da ya rubuta masa tun ranar Talata.

Ojuko dai sanar da cewa yayi murabus daga bisa kujerarsa saboda mtasalar dake faruwa a karamar hukumar Odo/Ota na jihar Ogun.

Tirkashi: Wani kwamishina yayi amai ya lashe a jihar Ogun

Cif Jide Ojuko
Source: UGC

KU KARANTA:Yan sandan Binuwe sun kama mutum 30 cikin mako guda

A wasikar da kwamishinan ya rubutawa gwamnan wacce ke dauke da kwana watan 14 ga watan Mayun 2019, magana take akan rashin amincewar kwamishinan akan matakin da gwamnan ya dauka akan wannan yanki, inda yake cewa ya ci karo da kudurin mutanensa.

Har ila yau, a cikin wasikar, ya nuna cewa abin da gwamnan yayi sam bai masa dadi ba. A don haka shi yayi murabus daga kan kujerarsa ta kwamishina. A daidai wannan lokaci abu mafi muhimmanci shine ya koma gida ya zauna da yan uwa da abokan arziki.

Bayan dukkanin wadannan bayanai dake kunshe cikin wannan wasikar, sai gashi kwatsam ranar Juma’a kwamishinan ya dawoma kujerarsa tareda cewa gwamnan yaki amincewa da murabus dinsa. Kuma matsalolin da yayi korafi ga gwamnan an mangancesu.

A wata zantawa da kwamishinan yayi da manema labarai ranar Juma’a cewa yayi, “ wannan wasikar tawa ba komi bace face wasikar nuna kauna tsakanin masoya biyu.”

Yace “ Gwamnan ya riga da yayi watsi da wasikar dana aika masa da ita cewa na ajiye aikina, wacce akayita yamadidi da ita a kafafen sadarwa.”

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

KU LATSA : Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadan

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel